Rabiu Ali Indabawa" />

IPOB Ta Bayyana Dalilin Arangamarta Da Sojoji

IPOB

A jiya ne ‘Yan asalin Biafra (IPOB) da aka haramta mallakar jiha, sun ba da hujja a kan rikici tsakanin jami’an tsaronta – kungiyar Tsaro ta Gabas (ESN) da sojoji.

Ta kuma yi ikirarin cewa an kashe wasu mazauna garin Okporo biyar a karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo lokacin da mutanen ESN suka yi artabu da sojoji a ranar Juma’ar da ta gabata. Duk da cewa Sojojin sun ce mutum daya ne ya mutu a cikin musayar wutar, IPOB ta dage kan cewa mutane biyar sun mutu wasu da dama kuma sun jikkata a artabun da ya barke tsakanin jami’an tsaron da sojoji da aka zakulo daga runduna ta 34 ta Artillery da ke Obinze.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta bakin kakakin IPOB Emma Powerful, kungiyar ta zargi Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma da aiki tare da Sojoji don kai hari tare da fatattakar jami’an ESN daga cikin dajin da suke aiki.
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatan ESN suna cikin daji suna bin ‘yan ta’adda da makiyaya wadanda ke can suna tsoratar da mambobinmu da ‘yan uwanmu a gonakinsu, ba hukumomin tsaron Nijeriya ba amma suna neman sanya mu cikin matsala.
“Tun lokacin da babban shugabanmu, Mazi Nnamdi Kanu ya kafa ESN da kuma rantsar da shi, a ranar 12 ga Disamba, 2020, suna cikin daji; aikinsu shi ne kare manoma daga maharan da suka yi sanarwar cewa duk filaye a Nijeriya nasu ne. “Kowane lokaci, Sojojin Nijeriya da ‘yan sanda za su zo su nemi matsalarsu a cikin daji,” in ji shi, ya kara da cewa kungiyar za ta sake duk wani kokarin murkushe mambobinta.
Ya zargi wasu shugabannin Kudu maso Gabas, ciki har da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma da sajewa da sojoji don kai wa ESN hari. Powerful ya ce mambobin kungiyar IPOB din da aka haramta basu gamsu da dokar hana fita 6 na yamma zuwa 6 na safe da gwamnan ya ayyana ba.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa Oguwike, ya ce an bayyana dokar hana fita zuwa wayewar gari ne bayan wani rahoto mai tayar da hankali kan ayyukan wasu gungun ‘yan bindiga da suka tayar da rikici a kan mazauna garin Orlu.

Exit mobile version