Connect with us

KASASHEN WAJE

Iraki Ta Kaddamar A Sabon Farmaki Kan Mayakan IS A Siyria

Published

on

Rundunar Sojin Iraki ta kaddamar da farmakin jiragen yaki kan mayakan kungiyar IS da ke cikin Siriya. Rundunar sojin Iraki ta ce an kaddamar da sabon farmakin ne bisa umarnin da amincewar Shugaban Siriya Bashar al-Assad da kuma rundunar sojin da Amurka ke jagoranta wajen yakar kungiyar ta IS. Iraki dai na da kyakkyawar dangantaka da kasashen Iran da Rasha, wadanda suka kasance manyan kawayen shugaba Bashar Al’Asad, zalika a lokaci guda, Iraki na samun goyon bayan hadar rundunar sojin da Amurka ke jagoranta a kasar ta Syria.

A watan Disambar bara Fira Ministan Iraki Haidar al-Abadi ya sanar da murkushe mayakn IS a fadin kasar, to sai dai mayakan sun ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake cikin kasar ta Iraki, daga maboyarsu da ke kan iyakarta da Syria

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: