Irin Asarar Da Rikicin Catalan Ya Haddasa

Ministan harkokin wajen kasar Spain Luis de Guindos ya yi ikirarin cewar rikicin yankin Catalonia ya haddasa wa kasar asarar sama da Yuro biliyan guda.

Rikicin a cewarsa ya kawo cikas ga tattalin arzikin yankin, wanda ya yi suna kan yawan masana’antu.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce, kididdiga ta nuna cewa tattalin arzikin kasar ya fado kasa da akalla matakai 5 daga inda ya ke a farko kan ma’aunin GDP kafin barkewar rikicin.

De Guindos ya ce rikicin ya sanya fiye da manyan kamfanoni da bankuna 1,300 janye hada-hadarsu daga yankin, matakin da ya haddasa rashin aikin yi ga dimbin jama’ar kasar.

Ministan ya dora alhakin matsalar ne a kan tsohuwar gwamnatin Catalan, wadda ya ce ta haifar da rashin tabbas da damuwa a yankin

Rikicin na Catalonia ya samo asali ne a lokacin da yankin ya bayyana ‘yancin kansa daga Spain a cikin watan Oktoban bara, bayan da gwamnati ta haramta yin zaben raba-gardama a yankin.

Exit mobile version