Kafin mutum ya yanke shawarar yin aure ya kamata ya bi matakai guda uku, na farko ya yi istikharah wato neman zabi daga wurin Allah, kamar haka; da fari mutum zai yi Sallah raka’a biyu kamar yadda ya zo a Hadisi, bayan ya yi sallama (wasu malamai suna ganin za a iya yin wannan addu’a kafin sallama), wato addu’ar neman zabi daga Allah, ko kuma mika wa Allah lamarin.
Mataki na biyu. Ya nemi shawara daga masana addini da dabi’u da halayya da gogayya da harkokin aure, domin su ba shi shawara bayan sun saurare shi sun ji irin tasa bukatar, wanda yake shawara ba zai yi nadama ba.
Mataki na uku.
Dole mai neman aure mace ko namiji su cire son zuciya idan su na neman aure nagari, duk da shari’a ba ta yarda mutum ya auri matar da baya so ba, amma mafi yawan mata na gari ba su fiya kyau da yawa ba, said ai hakan ba ya nuna cewar babu matar kirki a kyawawa, don haka idan an samu mace mai kyau amma ba ta da tarbiyya, sai kuma aka samu mai riko da addini kuma mai tarbiyya kuma tana da karancin kyau, sai ka ga an raba hankalin mai neman aure.
Ana auren mace saboda abu hudu, na farko; saboda kyawunta, na biyu saboda kudinta, na uku saboda nasabarta, na hudu saboda addininta.
Ma’akin Allah ya ce zai fi kyau ka auri ma’abociyar addini, idan ka ki hannun ka ya yi turbaya.
Wadannan abubuwa guda hudu su ne mafi yawan masu neman aure suka fi bukata ga mace, amma ana samun wata ta hada dukkan wadannan suffofin, wata kuma ta sami uku daga ciki, wata ta sami biyu wata ma suffa daya kawai take da ita daga cikin wadannan siffofin.
Wacce ta fi ita ce wacce ta hada dukkan wadannan suffofin:
– Mai kyau, mai kudi, mai nasaba, mai addini dukkan hudun tana da shi.
– Mai addini da kyau.
– Mai matsayi da kudi amma babu kyau babu addini.
– Mai addini amma babu kudi.
– Kyakkyawa amma babu tarbiyya ta addini.
– Mace tana da suffofi guda biyu na fili kamar kyau da muni ko baki da fari ko tsawo da gajarta, a kwai kuma suffofi na boye kamar kirki da hakuri da tarbiyya da juriya da iya zaman aure.
Mafi yawan mutane sun fi son mace mai kyau, hakan kuwa ba laifi bane, amma idan mutum ya auri mace saboda kyawunta kawai, lokacin da kyawun ya tafi, sai ka ga mace tana samun canji daga mijinta, saboda abin da ake son ta saboda shi ya tafi ko ya kare kuma mace mai kyau kawai babu tarbiyya sun fi wahalar da mazansu da halakar da su, domin za su rika yin abin da bai kamata ba.
A wasu lokuta domin su faranta musu ko da hakan ya sabawa Allah da Manzonsa.
Kowa cikin masu neman aure daga cikin maza ko mata akwai suffofin na fili da yake sha’awa daga matar da yake so ya aura, ko daga mijin da take so ta aura, kamar fara ko baka, doguwa ko gajeriya, mai kiba ko siririya, kyakkyawa ko mummuna, amma shi kyau da muni ya dangana ne da abin da mutum yake so, domin mummuna a wajen wani kyakkyawa ce, kuma kyakkyawa a wajen wani mummuna ce.
Mace mai tarbiyya de ita ce abin nema, idan ka samu mai tarbiyya kuwa ka gama more rayuwar aure.