Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home TATTAUNAWA

Irin Shugabancin Da Za Mu Yi A Sakkwato Ta Arewa – Hon. Mustapha Shehu

by Sulaiman Ibrahim
March 26, 2021
in TATTAUNAWA
4 min read
Irin Shugabancin Da Za Mu Yi A Sakkwato Ta Arewa – Hon. Mustapha Shehu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tsohon dadadden dan jarida ALHAJI MUSTAPHA SHEHU, mataimaki na Musamman ga Gwamna Tambuwal, shi ne dan takarar Jam’iyyar PDP a Shugabancin karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa a zaben da za a gudanar a gobe Asabar. Dattijon dan jaridar wanda ya taba zama Kakakin Gwamnatin Attahiru Bafarawa ya bayyana abubuwan da zai baiwa muhimmanci da fifiko idan Allah ya tabbatar da shi a wannan matsayin kamar yadda ya bayyana a wannan tattaunawar da wakilinmu SHARFADDEEN SIDI UMAR kamar haka….

Jam’iyyar PDP ta kaddamar da kai a gangamin taron da aka gudanar yau a matsayin dan takarar Shugabancin karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa. Ko wadanne irin ayyuka za ka fara idan ka shiga ofis?

karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, karamar Hukuma ce da ke cikin kwaryar Birnin Sakkwato wadda ke da iyaka daya da Gwamnatin Jiha. Idan a ka yi maganar shimfida hanyoyin mota, Gwamnatin Jiha ta samar da wadatattun hanyoyi, idan ka yi maganar asibitoci, kusan dukkanin manyan asibitoci suna nan a Sakkwato ta Arewa, haka ma a fannin samar da ruwan sha, akwai babbar tashar samar da ruwa a cikin wannan karamar Hukuma, bugu da kari idan muka yi maganar tsaftace muhall, Ma’aikatar Kula da Muhalli ta na gudanar da wannan aikin.

A fannin kiyon lafiya, akwai manyan asibitoci kamar yadda na bayyana, amma akwai kananan asibitoci da ke bukatar kulawa wadanda mafi yawa suna a cikin mawuyacin hali kamar yadda na ga wasu da ido na da kuma wadanda na ji labarin yanayin da suke ciki.

Aiki na, na farko in sha Allah shi ne ziyarar wadannan asibitocin na kiyon lafiyar al’umma a matakin farko domin gani da ido na ainihin zahirin yanayin da suke ciki domin sanin abin da karamar Hukuma za ta yi ta inganta ayyukan su.

Baya ga wannan, za mu bayar da kulawar musamman wajen karfafawa mata domin su zamo masu dogaro da kai ta hanyar samar da cibiyoyin horas da sana’o’i a wurare da dama domin mata su samu horon mabambantan sana’o’i da za su iya rike kansu da iyalansu.

Idan muka koma a bangaren ilimi, muna da Hukumar Bayar da Ilimi Bai daya da Hukumar Bayar da Tallafin Karatu wadanda ke bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci-gaba da bunkasar sha’anin ilimin al’ummar mu wanda duk da haka akwai kawance a tsakanin mu, za mu yi aiki tare, mu tabbatar wadanda ke da matsaloli mun taimaka masu tare da tabbatar suna shiga makarantu da kula da karatun su.

Duka baya ga wannan, fannin aikin gona, fanni ne da ba za mu yi kasa a guiwa wajen bunkasa shi ba, za mu tallafawa manoma musamman a noman rani wanda idan muka karfafa shi amfanin da za a samu ba kadan ba ne. A takaice da yardar Allah, za mu gudanar da mulkin gaskiya, adalci da ci-gaban al’umma.

Ko wane kokari za ku yi a fannin kula da haraji domin ganin jama’a sun amfana da harajn da suke biya?

Sha’anin karbar haraji yana da matukar muhimmanci don haka za mu ba shi kulawar musamman domin duk abubuwan nan da na fada, za su tabbata ne kawai idan akwai kudin gudanarwa, don haka za mu yi kokarin duk wani waje da haraji ke shigowa mun kula da shi ya kuma shiga asusun karamar Hukuma tare da toshe sulalewar haraji. Za mu yi amfani da kudaden shigar da muke samu wajen aiwatar da ayyuka da shiraruwan da al’umma za su amfana ta yadda za su ga zahirin abin da aka yi masu da kudaden su wanda hakan zai kara karfafa masu guiwa wajen biyan haraji.

Akwai korafin yawaitar ma’aikatan bogi a kananan Hukumomi, ko wane mataki za ku dauka domin magance wannan matsalar?

Wannan matsalar ai Gwamnatin Jiha ta riga ta dauki matakin magance ta, ta hanyar gudanar da aikin tantance ma’aikata wanda an riga an yi a Sakkwato ta Arewa a watannin baya tun a tashin farko, kuma za mu yi amfani da wannan aikin, wadanda aka tantance suke cikin albashi, ba za mu taba kowa ba domin an riga an tantance su a matsayin sahihan ma’aikata, wadanda kuma aka riga aka cire ba za mu dawo da su ba, domin an taskace su a matsayin ma’aikatan bogi. Maganar ma’aikatan bogi ta zo karshe domin babu wani aboki na, ko abokan siyasa ta ko wani na kusa da ni da za mu baiwa gurbin ma’aikatan bogi, dukiyar jama’a ce kuma za a yi masu aiki da ita don haka su kansu jama’a ma ba za su yadda mu yi hakan ba.

Sakkwato ta Arewa karamar Hukuma ce da ke da kalubale. Ko wani shiri ka yi domin ganin ka sauke nauyin da aka dora maka?

Alhamdulillahi na shirya sosai. Hasalima a ranar da wannan takarar ta tabbata, mutum na farko da na fara kira shi ne abokina Kabiru Assada, Babban Editan Muryar Arewa wanda a lokacin yana Kaduna, na fada masa cewar muna cikin tsaka- mai- wuya domin ga kalubalen da ke gaban mu, daga lokacin abubuwa da dama sun faru. Mutane da dama sun bayyana ni a matsayin mutum mai gaskiya da amana da aiki tukuru, wanda shi ne kalubalen da ke gaban mu wajen tabbatar da gaskiya da adalci, don haka ne na ce mun shirya. A wannan shugabancin a kodayaushe kungiyar ‘Yan Jarida na zuwa a raina, idan na yi ba daidai ba, za a soki ‘yan jarida a ce sun kasa, za a zargi abokai da ‘yan uwa na, amma idan na yi abin kwarai, na sauke nauyin da ke kaina, ‘yan jarida ne za a yabawa har gobe a sake kiran wani dan jarida a dora masa nauyin shugabancin al’umma domin sun yi an gani an yaba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Auren Da Nake Muradi

Next Post

Yadda Nagartattun Al’adu Da Tunanin Da’a Na Kasar Sin Suka Ba Da Jagoranci Ga Ladabin Al’ummarsu (2)

RelatedPosts

Gari

Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Sun Amince Da Takarar Hon. Yusuf Salihu Shaka -Muntaka Umar Jega

by Muhammad
4 days ago
0

Editanmu Bello Hamza ya tattauana da Malam Muntaka Umar Jega,...

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

by Daurawa Daurawa
4 days ago
0

A cikin wannan hira za a ji yadda manyan 'yan...

NIRSAL

Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Mazauna Abuja, Ya Yabawa Manajan Daraktan NIRSAL

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Mataimakin shugaban yan kasuwar na Arewacin Nijeriya, wato ‘Arewa Traders...

Next Post
Yadda Nagartattun Al’adu Da Tunanin Da’a Na Kasar Sin Suka Ba Da Jagoranci Ga Ladabin Al’ummarsu (2)

Yadda Nagartattun Al’adu Da Tunanin Da’a Na Kasar Sin Suka Ba Da Jagoranci Ga Ladabin Al’ummarsu (2)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version