Connect with us

Uncategorized

Irin Sirrukan Dake Tattare Da Sana’ar Gyaran Mota –Injiniya Dalladi

Published

on

Babu ko shakka babbar matsala matasan yau ke ciki na sakaci ko kuma rashin mayar da hankalinsu ga koyon sana’o’in dogaro da kai da zasu iya tunkarar duk wata kalu-bale da za ta taso ma su a gobe, wato a lokacin da za su kasance ana jiransu domin su warware matsalolin da za su taso ma su girma ya dabaibaye su. Wakilinmu da ke Zariya BALARABE ABDULLAHI, ya sami dammar zantawa da wani fitacce kuma gangarau a fagen gyaran mtoci mai suna INJINIYA DALLADI, wanda aka fi sani da DALLADI INBESTMENT, da ke gudanar da sana’ar gyaran motoci a kan kwanar Unguwar Kaya, a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.A zantawar da wakilinmu ya yi da wannan bawan Allah ya bayyana matsalolin da ya fuskanta a lokacin ya na koyon gyaran mota ya zuwa halin da ya ke ciki a yau. Ga yadda tattaunawar ta kasance da Injiniya Dalladi.

Yaushe ka fara koyon sana’ar gyaran mota?
A gaskiya iyaye na sun taba shaida ma ni t un ina dan shekara goma aka sa ni a gareji, domin in koyi gyaran mota, Kuma, da sassafe sai na je makarantar Allo, in rana ta fito kuma, sai in je makarantar boko, da zarar na dawo makarantar boko sai in wuce wajen gyaran mota.
Me za ka iya tunawa na yadda ka sami goyon baya daga iyayenka?
Babu ko shakka nib a abin d azan ce wa iyayenmu sai dai godiya domin sun yi ma ni duk tsarin da rayuwa ta za ta yi kyau, domin kamar yadda na fada ma ka, a duk rana ba ni da lokacin yin wasa ko kuma zuwa filin kwallo da dai sauran wasanni, dmin na bayyana ma ka yadda tun da safe na ke zuwa makarantar Alloy a zuwa makarantar boko sai zuwa wajen koyon gyaran mota.
Kuma zan iya tunawa, wannan tsari da iyaye na suka yi ma ni, tare da ddu’ar da suke yi ma ni, ban san wata rana d azan ce na tashi makarantar boko na wuce wajen wasa ba, duk wani motsi da na ke yi, sai in ga kamar suna gani na ne, sai na mayar da hankali ga wannan hanya ta
gyaran moto da suka sa ni.
Ga abokan ka, me za ka iya tunawa a wancan lokaci?
Wannan wani abu na musamman da ba zan taba mantawa da shi ba, domin a lokacin da na ke koyon gyaran mota, abokai na a duk rana in na sa kayan gyaran mota, da zarar sun yi arba da ni, dariya suke yi ma ni, na farko, ba ni da lokacin wasa ko kuma hira a cikin ‘yan uwana matasa, sai in sun ganni babu abin da suke yi ma ni sai zunde na da kuma aibanta ni, saboda ba ni da lokacin wasa da su suke da shi.
Ka taba samun kan ka a cikin horo daga wadanda suka koya ma ka wannan sana’a ta gyaran mota?
To, ka san shi horo ana yi wa mai laifi ne ko kuma mara jin Magana, in ko wadannan dalilai ne za su sa ayi ma ni horo ko kuma hukumci, to tun da farko na shaida ma ka tsarin da iyayenmu suka yi ma ni, Allah ya taimake ni, na bi tsare-tsaren da na bayyana ma ka a baya da iyayenmu suka ni a kai, na kuma ce ma ka Allah ya yi ma ni jagora, yanzu sai godiya na ke yi a dare da kuma rana.
To a lokacin da ka fara koyon gyaran mota, me za ka iya tunawa na nau’in motocin da ake gyara wa a wancan lokaci?
Wadanda suka koya ma ni gyaran mota, suna gyara motoci iri daban-daban, amma a cikin ikon Allah, a yau al’umma sun ni gwani ne a fagen gyaran motar firjo, baya ga sanin da na yi wa wannan mota na kuma tsaya na koyi gyran firjo kamar yadda na bayyana ma ka na iya gyara mota kirar Honda, to ka ji inda na sa ni, wato motoci biyu.
A lokacin da ka ke koyon gyaran mota, wasu hanyoyi ake bi a gane ka iya gyaran da ake koya ma ka?
Akwai hanyoyi da yawa, hanya ta farko ita ce, irin mayar da hankalin ka, wanda yake koya ma ka gyaran zai fara umurtar ka ka yi wasu abubuwa a gabansa, daga nan sai ya fara tura ka ka dauko mota a wasu wurare da ta lalace, ko kuma ya ce je wani waje ka gyara wata mota da ta lalace, ihar dai zuwa lokacin da mai gidanka zai ce ya ‘yanta, ka je ka bude inda za ka yi gyara, in kuma ya ‘yanta ka, zai hada ka wasu yara su kasance a karkashinka, wato ka ci gaba da koya ma su sana’ar gyaran da aka koya ma ka.
Zuwa yanzu, kai ma koya wa wasu matasa wannan sana’a ta gyaran mota kuwa?
Lallai na koya ma su, ban ma san yawansu ba, kuma a halin yanzu, wasu na yin gyaran a ciki da wajen jihar Kaduna, wannan ne ya sa yanzu na fara bude wuraren gyaran motar Firjo a wasu jihohin Nijeriya ban an jihar Kaduna kawai ba?
Ko ka na da shawarar da za ka ba iyayen yara na ganin yaransu sun sami sana’ar dogaro da kai da zai tsirar da su daga tsunduma balbalcewa?
Babban shawarar ita ce, an ce gani ga wane-ya isa wane tsoron Allah, yadda yara suka lalace a yau, hakan ya faru ne a dalilin rashin abin yi da za su dogara shi.zai kyau iyaye su sa yaransu a sana’a, kuma in sun sa su, su rika samun lokacin da za su rika zuwa wajen da yaransu ke koyon sana’ar, ya na kara wa wanda ke koya wa yaran sana’ar ya kara azzamar rungumar yaran da hannu biyu.
A karshe wannan sana’a ta yi ma ka asin-da-asin kuwa?
(Alhamdu-lillahi), wannan sana’a ta gyaran mota ta yi ma ni duk abin da dan adam yake bukata ya rayu, kuma ta kai kasashe da yawan gaske ciki har da sauke farali a kasa mai tsarki da duk musulmi ke son ya je.Babu shakka, ina godiya ga Allah da ya ba ni ido a wannan sana’a, sai iyaye na da suka sani a wannan hanyar da tabbatar ma ka ta zama alheri a gare ni, alheri kuma ga wadanda na koya ma su ko kuma na ke koya ma su a halin yazu, ba zan kammala ba, sai na nuna farin ciki ga ma su gida na da suka koya ma ni wannan sana’ar, Allah ya yi ma su tukuici da Aljanna-Firdausi, amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: