Dan wasan Real Madrid Isco, ya amince ya ci gaba da taka leda a kungiyar har na tsawon shekara biyar.
Dan wasan tawagar Spaniya mai shekara 25, wanda ya ci wa yi wa Madrid kwallo 34, zai ci gaba da zama har zuwa karshen kakar wasan shekara ta 2021 zuwa 2022.
Isco ya lashe kofin zakarun Turai uku da na La Liga daya da Copa del Rey tun lokacin da ya koma Bernabeu daga Malaga kan fam miliyan 23.
Dan wasan shi ne na biyu da ya tsawaita yarjejeniyarsa da Madrid a makon nan, bayan dan kwallon tawagar Brazil, Marcelo.