Akalla mutane 74 ne suka rasa rayukansu wani kazamin harin bom da bindiga da aka kai kusa da birnin Nasiriyah da ke kudancin Iraki. Haka zalika da dama sun samu raunuka a harin wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.
Mataimakin shugaban sashen kiwon lafiya na lardin Dhikar da ke birnin Nasiriyah, Abdel Hussein Al-Jabri, ya shaidawa Kamfanin dilancin Labaran Faransa na AFP, cewa yanzu haka akwai sama da mutane 87 da suka samu munanan raunuka a harin bayan wadanda suka rasa rayukansu.
Haka kuma ya bada tabbacin cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutun ya karu nan da wani lokaci idan aka yi la’akari da munanan raunukan da suka samu.
Al-Jabri ya kuma bayyana cewa yanzu haka zaman lafiya ya fara dawowa yankin da lamarin ya faru, bayan da aka kwashe gawakin majinyatan kuma aka garzaya da su asibitoci don karbar kulawar gaggawa.
Bama-bamai Sun Tashi A Kasar Ingila
Wasu tagwayen bama-bama sun tashi a birnin Landan na kasar Ingila, sai dai babu rahoton mutuwar mutane, amma mutane akalla 22 sun ji munanan raunuka.
Fira ministar Britaniya, Theresa May ta ce za a ci gaba da karfafa tsaro a kasar sakamakon harin da aka kai wanda ya yi sanadiyar raunata mutane akalla 22.
Rundunar ‘yan sanda a Britaniyan ta ayyana harin a matsayin na ta’addanci inda ta shawarci al’umma da su guji zuwa wurin da aka samu fashewar da ta haifar da rud
ani a tashar jirgin a ya yin bincike gano wadanda suka kai wannan harin.
Magajin garin birnin Landan Sadik Khan a jawabinsa ga manema labarai bayan aukuwar lamarin ya yi alla-wadai da abinda ya kira ayyukan muggan mutane da ke amfani da ta’addanci domin hana al’umma walwala, karo na biyar kenan da ake kai wa Britaniya hari a cikin wannan shekara ta 2017.