A kalla mutum Uku ne suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar iskar gas a garin Kabba dake Jihar Kogi a yammacin jiya Laraba.
Wakilinmu ya nakalto daga wasu shaidu cewa lamarin ya faru ne a wata matattaran shan barasa dake kusa da mahadar Lewi a garin na Kabba da misalin karfe 9:45 na maraice.
“Naji kara mai karfin gaske, nan da nan na isa inda lamarin ya afku inda na hango mutum Uku a kwance ko motsi basa yi, a yayin da kuma aka garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa babban asibitin St. John dake Kabba domin karbar magani” Inji majiyar.
Wani kuma dan Acaba wanda shima ganau ne mai suna Dele, ya bayyana lamarin da cewa fashewar bam ne, inda ya bada hujjarsa da cewa karar fashewar da mutum uku da suka rasu da kuma wadanda suka jikkata, alama ce na fashewar bam.
Sai dai kuma kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Edward Egbuka wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace fashewar gas ne ba bam ba ne kamar yadda wasu ke tunani.
Kwamishinan ‘Yan sandan ya kuma ce jami’ansa na kan binciken lamarin,inda ya kara da cewa zai yi karin bayani akan fashewar bayan kammala binciken lamarin.