Ista: CAN Ta Bukaci Kiristoci Su Yi Koyi Da Koyarwar Almasihu

Ƙungiyar Kirista ta Nijeriya (CAN), reshen jihar Ogun, ta bukaci Kiristoci da shugabanni na siyasa da suyi koyi da koyar war Almasihu, kama daga kan hakuri bada hadaya kyautata mutane kai wa juna ziyara ranar Easter.
Fasto Tolulope Taiwo, wanda ya fadi hakan lokacin da yake bayani ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a garin Abeokuta a ranar Lahadi.
Taiwo ya lura cewa Easter wani muhimmin abu ne a wajen Kirista wanda ke koyar da su kyawun dabi’u, duk kan wani Kirista ya tashi ya nemi gafara domin Allah ya ya fe masa zunuban sa da ya aikata. “
Ya kuma gargadi Kiristoci da su guji aikata laifukan da zasu samu zunubi a daidai wannan lokacin, kyawawan dabi’u su ne zasu kasantar da mutum zuwa ga ubangiji Allah. “
“Ana ganin mutuwar Yesu a matsayin mai ma’ana a gare mu cewa ba mai zunubi bane shi, mai tsoron Allah ne ya kamata muma mu yi koyi da rayuwar sa mai tsarki”
“Wannan darasi ne na bikin da muke yi mu Kiristoci bawai dan kauna ba kawai.Littafi mai tsarki ya ce idan Yesu bai tashi ba
ba za a rasa ciwo ba, “inji shi.
“Shugabannin siyasarmu ba za suyi aiki ba ne kawai don kansu,
ya kamata su san cewa suna aiki ne ga yan kasa wadanda hakin su ya ke kan su. “
“Dole ne su sadaukar da komai nasu ga talakawan da suke mulka kana su kuji cin hanci da rashawa wanda shine babban abinda yake durkusar da tattalin arzikin kasa. “
Bugu da ƙari, ya umurci dukan Kiristoci su yi wani aiki wanda zai sa a rinka tunawa da su sabida haka ne koyarwar Almasihu.

Exit mobile version