Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce kungiyar ISWAP ta kai harin kwanton bauna ga kwambar motocin sojin Nijeriya, inda ta kashe soja biyar, tare da sace fararen hula. Ya ce an far wa kwambar motocin sojin ne kwana guda bayan ‘yan ta-da-kayar-bayan sun auka wa matafiya a wannan yanki, tare da sace mutum 35, bayan kashe wata mata.
Harin na da aka kai a wajen Mafa, shi ne na baya-bayan a hare-haren da ‘yan ta-da-kayar-bayan suka kai a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas. Ko a karshen makon da ya wuce masu ikirarin jihadin sun sace matafiya 35 a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri. Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun ce, marahar sun sanya shinge ne irin na jami’an tsaro suka rika fito da mutane daga motocinsu, kuma suka harbe wata mace guda har lahira.
Hare-hare da garkuwa da mutane na kara zafafa a Arewacin Nijeriya, duk da ikirarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa tana cin galaba kan yaki da masu ta-da-kayar bayan. Kuma harin baya-bayannan da ya fi jan hankali har ya janyo kakkausar suka ga gwamnati shugaba Buharin shi ne na yankin Zabarmari a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas, a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka dira yankin, suka kashe manoma 42 ta hanyar yi musu kisan gilla.
Majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda kungiyar Boko Haram ta yi wa kisan gillar a Zabarmari sun haura mutum 100. Ko a makon da ya gabata mahara sun sace ‘yan makarantar sakandaren kwana da ke garin Kankara su sama da 300 a Jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma, duk da an yi nasarar karbo su a karshen makon. Ko shekaran jiya Asabar ‘yan bindiga sun yi yunkurin sace wasu mata ‘yan makarantar Islamiyya su 80 a garin mahuta duk dai a jihar ta Katsina, wadda ita ce mahaifar shugaban Nijeriyar Muhammadu Buhari.