Connect with us

NOMA

ITEC Za Ta Ta Yi Hadin Gwiwa Da Kungiyar Masu Surfe Da Nika A Neja

Published

on

Kamfanin ITEC Engineers da ke minna ta sha alwashin samar da injimukan surfe da sarrafa garin masara ga mambobin kungiyar masu surfe da nika a jihar Neja, jami’in hulda da jama’a na kamfanin ne ya bayyana wa manema labarai bayan wani zama da aka yi tsakanin kamfanin sa da kungiyar lahadin nan da ta gabata a minna.
Jami’in, Abubakar Ma’ajin , yace ganin gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen bunkasa kananan sana’o’i dan anfanar jama’a yasa kamfanin sa mayar da hankali wajen kera injimukan surfe da nika da kuma hako ma’adinan kasa, yasa suka ga dacewar hada hannun da wannan kungiya dan samar masu injimuka masu nagarta kuma da aminci a cikin saukin farashi.
Bayan sayarwa a saukake mune zamu dauki nauyin gyara masu idan an samu matsala, muna da burin hada su da bankuna dan ba su rance da kuma ‘yan kasuwar da zasu tallata masu hajarsu a inda ya kamata. Ganin cewar akwai talakawa ko in ce marasa karfi da ke muradin yin wannan sana’ar in har kungiya za ta tsayawa mutum mu a shirye muke wajen bada bashi da kuma tsara hanyoyin da kudaden mu zasu fito ba tare da wata matsala ba.
Ina baiwa wannan kungiya tabbacin cewar indai bashin kayan aiki ne ba kudi kasa ba a shirye muke mu ba su, domin abinda ke jawo matsala a harkar bashi bai wuce bada kudi kasa ba, mu kaya zamu bayar kuma zamu tsara hanyar yadda za a biya, ina indai shugabannin da mambobin kungiyar sun hada kai za a anfani juna.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban kungiyar masu surfe da nika ( Millers Granding ) ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta, yace lallai bayan zuwan ITEC wannan kungiya sun yi rajista da mu, kuma sun muna alkawalin samar mana da injuna masu karfi da nagarta, na banbaran masara, tatsan man kuli-kuli da kuma na nikan tumatur, sun mana wannan alkawalin kuma mun gode masu zamu shiga yadda zamu tattaunawa da su.
Da farko dai sun yi rajista da mu, abu na biyu sun fada mana zasu hada da babban bankin Najeriya, domin su san matsayin mu da irin taimakon da zasu rika ba mu, da kuma bankin masana’antu. Abu na uku kuma shi ne zasu taimaka mana wajen tallata hajar mu, domin muna son zasu fara yin garin masara a cikin buhu ko laida wanda zai saukakawa magidanta wajen bin layin nika musamman a manyan garuruwa, sun sha alwashin hada mu da kwararru wajen hada sitaci da yadda za a rika gyara shinkafa ta yadda za ta kara inganci, dan haka muna kyautata zaton zamu gajiyar wannan shirin in Allah Ya yarda.
Ganin yadda aikin kungiyar ya kankama mun fara shirin fadada tafiyar, domin mun fara zama da mutanen Kebbi, Sokoto, Kaduna da Nasarawa, ina sa ran nan gaba kadai za a samu karin jahohi ta yadda zamu gajiyar wannan shirin tare.
Shugaban ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da na jahohi wajen inganta watan lantarki a kasar nan, yace babban kalubalen da manya da kananan masana’antu ke fuskanta yanzu bai wuce maganar wutan lantarki ba, wanda duk irin yunkurin da za ka yi na inganta sana’a musamman wanda injin ne zai buga shi in har ba a samu wutan lantarki wadatacce kuma cikin saukin rahusa ba, ba yadda za a sana’ar ka ta bunkasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: