Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Wani Matashin dan siyasa a karkashin jam’iyyar PDP a jihar Katsina mai suna Alhaji Bishir Biro Kankia ya bayyana cewa gwargwadon yadda ka taimakawa jam’iyyar APC ta dare karagar Mulki to gwargwadon yadda kake shan wuya a wannan lokaci.
Bishir Biro Kankia ya yi wannan furucin ne a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan bision FM Rediyon Katsina a cikin shirinsu na kowane tsuntsu… wanda kuma haka yana daga cikin martani da ya mayar wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suke cewa PDP ta yi barna a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulki.
Inda ya bayyana wasu ayyuka da suka yi tare da kalubalantar ma su cewa barna jam’iyyarsu ta tabka a lokacin da suke kan mulki. Wasu daga ayyukan da ya bayyana sun hada da Biyan kudin jarabawa da gina baban titin da ya kewaye garin Katsina da gina sabon gidan Gwamnati da gina jami’ar Umaru Musa Yar’adua da gida Asibitin kashi da gina filin sauka da tashin jirage da gina Babban filin wasa da kuma sakatariya gwamnatin jihar Katsina.
Ya kuma kara bayyana dalilinsa na cewa gudumawar da ka bada ita gwargwadon wuyar da kake sha, ya ce lokacin Jonathan kudin Hajji dubu dari bakwai yanzu miliyan da rabi kudin Man fetur 86 yanzu 145, ya kara da cewa da Jonathan ne yake mulki kuma ya kara wadannan kudadan da har gida za a bi su ana jifa amma yanzu ga shi Musulmi ne ke Mulki amma an yi shiru.
Mu da ake ganin idan jam’iyyar APC ta hau mulki za a yi wa rigunar gamin baki za mu saki matanmu saboda wuya to yanzu duk inda ka ga mutum da komari yana da kwanciyar hankali to dan PDP ne, inji Bishir Biro.
Ya kara cewa babban abinda ya burgeshi game da wannan mulki na jam’iyyar APC shi ne malamai wadanda suka rika shiga Masallaci suna kafirtasu idan sun tafi zabe suna yi masu kabbara, yau sai gashi ana musayar wuta tsakanin wadannan Malamai da gwamnatin su da aka ce ba mu da tsarki suna da najasa.