Connect with us

LABARAI

‘Iyalan Abacha Suka Bai Wa Buhari Dogari Marigayi Lawal Mato Ba ‘Yar’adua Ba’

Published

on

Iyalan Marigayi Janar Sani Abacha sun bayyana cewa tsohon Dogarin Buhari da ya rasu wato Marigayi WO Lawal Mato, Iyalan na Abacha ne suka bai wa Buhari shi tun shekarar 2003 domin ya zama masa jami’in tsaronsa.

Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwa da Alhaji Bilyaminu Yusuf, mataimaki ga Hajiya Maryam Sani Abacha ya fitarwa da manema labarai a Kano a ranar Talata.

Alhaji Bilyaminu Yusuf, ya ce wannan bayanin ya zama wajibi ne su yi shi ne a daidai wannan lokacin domin ganin yadda Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya jirkita tarihi yadda abin yake, inda ya tabbatar da cewa Iyalan Abacha din ne suka mikawa Buhari Marigayi WO Mato tun kafin ma ya ci zaben 2015.

“Batun da Garba Shehu ya yi na cewa Mato (Marigayi) yana daya daga cikin tawagar da tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua ya bai wa shugaba Buhari a matsayin jami’in tsaronsa, ba kawai ba gaskiya bane, abu ne ma da ake neman sauya sahihin batu.” Inji shi.

A cewar Alhaji Bilyaminu Yusuf, akwai bukatar Kakakin shugaban kasar, Garba  Shehu ya gyara wannan kuskuren da ya yi domin gyara tarihi yadda yake.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya jikan Mato, ya sanya shi a Aljannah Firdaus, sannan ya bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Marigayi WO Lawal Mato ya rasu ne a ranar Talatar 21 ga watan Afrilun 2020, bayan ya yi fama da ciwon shuga har na tsawon shekara uku.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: