“Iyaye A Arewa Ku Ji Tsoron Allah Kan Sauke Hakkin Yaranku”

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.

A Arewa ne za ka samu gidan Almajirai da yara ba adadi, a Arewa ne za ka samu iyaye sun sake yaran su ana kwashewa ana sauya musu addini, a Arewa ne za ka samu gidan kangararru inda ake tara daruruwan yara wai da sunan sun gagari iyayensu.

Kwanaki kadan da suka wuce wata Baiwar Allah ta saka wani bidiyo a shafin sada zumunta na Twitter, inda yara mata kanana wadanda shekarunsu bai wuce 15 ba, suna neman a sanya musu alluran hana daukan ciki. A cikin bidiyon da aka tambaye su ko me za su yi da shi alhalin ba su da aure? sai suka ce talla ne aikin su. Matukar suka dawo gida ba tare da ciniki mai yawa ba, to korin su za a yi a gida.

Har yanzu jami’an tsaro ba su gama kwato yara da ‘yan kudu (kabilar ibo) suka wawushe daga Arewa ba. Wadannan yara an ci zarafin da yawa daga cikin su kuma an keta musu hadi. An tirsasa su bin addinin da ba su da alaka da shi.

Abin da zai ba ka mamaki shi ne, saboda tsabar rashin kula, iyayen wadannan yara ba su nemi yaransu ba lokacin da suka bata. Ba su hadu suka sami gwamnati a kan cewa ana kwashe musu yara ba tare da sun san su waye ba. Taimakon Allah ne kawai ya sa aka kama barayin yaran. Idan da jami’an tsaronmu ba su kama su ba, to da shiru za ka ji.

Har ila yau, a Arewar mu ne aka bankado gidajen kangararru. Irin wadannan gidaje an yi su ne don karbar yara daga hannun iyaye da sunan sun kangare. Jami’an tsaro sun gano cewa ana ketawa yara hadi ta hanyar luwadi da su, hakazalika yaran na fama da cututtuka daban-daban.

Tambaya a nan shi ne, me ya sami iyaye a Arewa?

Ko iyaye sun manta cewa haihuwa kyauta ce daga Allah madaukakin sarki, wanda duk wanda aka ba shi to akwai hakkoki a kansa?

Ko iyaye sun manta cewa hakkin ciyar da yaransu, tarbiyyantar da su, tufatar da su, samar musu matsuguni da ba su ilimi duk ya rataya a wuyan su ne?

A kowani lokaci da iyaye suka yi wasa da hakkokin yaransu, to tamkar suna sake kuraye ne a cikin al’umma. Wadannan yara za su nemi su ci koda kuwa ta wani hanya ne. Za su nemi su sanya tufafi ko ta wani hanya, za su nemi su ji dadin rayuwa ko ta wani hanya.

Yaron da ya rasa samun hakkokinsa a wurin iyayensa to ya samu matsala. Ba zai iya fahimtar dai-dai da kuma ba daidai ba. Tunaninsa ya samu tasgaro, cikin lokaci karami zai iya zama bala’i a cikin al’umma.

Laifin waye?

Dukkan masu fada a ji ya kamata su ta shi tsaye, malamai da sarakuna su suka fi kusa da al’umma, dole su fadakar a kan wanann fitina da muka tsinci kanmu a ciki. Gwamnati dole ta fito da matakai masu tsauri a kan iyaye marasa tausayi da imani. Dole iyaye su kula da yaransu. Dole yara su samu kulawa daga iyayensu.

Sako daga Mahmud Isa, Yola.                                                                                                                           

08106792663

“Taya Murna Ga Gwarzon Namiji”

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. Edite ka bani da na taya Alhaji Malik Anas Katsina, murnar samun Akanta Janar wanda Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Rt Aminu Bello Masari, ya ba shi. A gaskiya Alhaji Malik Anas, mutum ne mai kamanta adalci mai taimakon al’umma da tausayin talaka, ina roko Allah ya taimaka masa domin zatinsa, amin.

Sako daga Saminu Mayentea Batsari.

08036773485

“Kira Ga Matasa Maza Da Mata Su Guji Fadawa Cikin Sha’awa”

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.

Babban abin da ke addabar matasa maza da mata shi ne, sha’awa. Kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani da muke ciki zai ga cewar da yawa wasu na fadawa cikin aikata fasikanci ba cikin son ransu ba, sai don abin ya fi karfinsu. Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron Allah, ya san illar zina, ya san girman zunubinta, amma saboda fitinar sha’awa ya ka sa daurewa har sai ya je ya aikata din. Wani haka zai ta aikatawa yana tuba da haka har zina ta zame masa jiki ya run ka ganin ai yinta ba komai bane.

Haka za ka ga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, ta san illar zina, ta san girman zunubinta amma sai fitinar sha’awa ta sa ta afka cikin wannan bala’i.

Domin kaucewa fadawa makaranatar Shaidan, dole ne duk wani matashi da yake fuskantar barazanar sha’awa ya yi la’akari da wasu dokoki da addini ya shar’anta masa, sannan kuma ya yi amfani da dabaru wanda za su taimaka masa. Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya take, daga cikinta take bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta taso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna.

To ya ake gyara zuciyar ?

Ana gyara ta ne ta hanyar cikata da kyawawan tunani da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta da goge mazaunin duk wani mummunan shauki. Daga nan sai kyautata dabi’u da halaye da ayyuka, duk wata dabi’ar wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai bamai kyau ba ne, to yin watsi da shi zai kara haskaka masa zuciyarsa. Kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimakawa ‘yan’uwa, makwabta da abokai, gaskiya da rikon amana da sauransu. Kyawawan ayyuka sun hada da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da aka sa ba dai-dai ba ne a addinance sai ayi kokari a barshi komai dadinsa ko ribarsa. Yawan sanya Allah a zuciya da yin zikiri. Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yake wa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa.

Lallai ne ‘yan’uwa mu kula da kiyaye sallolin farilla da nafila da yawaita karatun al-kur’ani da sauran azkar.

Sannan dole mu kiyaye maganar Manzon ALLAH (s.a.w), inda yake cewa, “ya ku matasa duk wanda yake da hali ko iko to ya gaggauta yin aure, wanda kuma ba shida halin yin aure, to ya yi azumi domin wannan yana da kushe kaifin fitinar sha’awa.”

Haka kuma dole su kansu iyaye su kula da rayuwar ‘ya’yansu matasa maza da mata, domin kare su daga wannan bala’i.

Sako daga Mahmud Sani, KD.                                                                                                                           

08151693170

Exit mobile version