Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
An yi kira ga iyaye, musamman mata dasu rage buri da kuma son abin duniya a yayin da aka zo neman yayansu mata da aure.
Wani malamin addinin musulunci dake garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, Ustaz Ahmad Tijjani Sarkin Noma ne yayi kiran a wajen walimatu Nika’in auren Mallam Abdullahi Abubakar Sha’aban da amaryarsa, Malama Khadijat Aliyu Abdullahi Dan Sokoto da kuma Mallam Abdulsalam Sha’aban da amaryarsa, Malama Khadijat Uthman wanda aka gudanar a gidan babban limamin garin Lokoja dake Unguwar Fawa a ranan Asabar data gabata.
Ustaz Ahmad Tijjani Sarkin kazalika ya bayyana cewa yawan zinace zinace na faruwa a tsakanin saurayi da budurwansa ne idan har suka dauki lokaci mai tsawo ba suyi aure ba saboda tsadar da auren ke da shi, wadda hakan a cewar malamin shike haifar da haihuwar shegu barkatai, lamarin dake haddasa masifu iri iri a doron kasa.
Ya kara da cewa” Zaka ga mutum jarinsa bata wuce naira 500,000 ba, amma Kuma sai kaga iyayen yarinya, musamman mata wai don yaje neman auren yarsu, sai su zayyano masa abubuwan da yafi karfinsa. A don haka nake shawartan iyaye mata da ku duba irin yanayin halin da ake ciki a wannan zamani na matsin tattalin arziki,ku rika sassautawa duk wanda yazo neman diyarku da aure. Ku rage yawan buri da son abin duniya a yayin da aka zo neman yayanku mata da aure. Ina mai tunatar da ku cewa aure mafi albarka shine auren da aka kashe dukiya mafi kankanta kamar yadda Annabi Muhammadu ( SAW) ya fadi”Inji Usta Tijjani Sarkin Noma.
Malamin har ila yau ya shawarci namiji mai neman aure da ya guji nuna karya ga yarinya ko iyayenta a yayin da neman aurenta,inda yace yin haka yana daya daga cikin abubuwan dake rusa auren koda an samu nasarar yinta,yana mai cewa karya fure take bata yaya.
A karshe Ustaz Ahmad Tijjani Sarkin Noma yayi wa angwaye da amarensu fatan samun zaman lafiya mai dorewa tare da yin kira gare su dasu suyi hakuri da junansu cikin zamantakewar auren.