Connect with us

LABARAI

Iyaye Ku Sa Ido Kan ’Ya’yanku –Misis Zira

Published

on

Misis Rhoda Zira Dia, ita ce mai bada shawari kan harkokin jinsi a kungiyar Mata ta Majalisar dinkin duniya da kula da Mata da kuma tsaro, ita ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a Gombe jim kadan bayan kammala wani taron jinsi da kungiyar ta UN Women ta shiryawa yan jarida a otel din Costodian dake Gombe.

Misis Rhoda Zira, tace a matsayin ta na ma’aikaciyar UN Women ta na mai bai wa Iyaye shawara kan bai kamata suna barin ‘ya’yan su suna yawo barka tai ba domin yanzu lokaci ya canja wanda aka yarda da shi shi zai shiga jikin ka ya rudi Yaran da suka saba da shi har ya yi musu fyade.

Ta kuma ce yanzu siyasa tazo barin yara suna yawo barka tai shi ke jawo a sace Yara a neme su a rasa ko a yi musu fyade ba tare da sanin Iyayen su ba saboda iyayen basu san halin da ‘ya’yan suke ciki ba dan haka take kira da a sa ido idan har an samu matsalar fyade kar a boye dan gudun cewa idan aka bayyana za’a tona asirin Yarinya da aka yiwa fyaden.

Rhoda Zira ta ce, idan aka bayyana ne Yarinyar da aka yiwa fyaden za ta samu taimakon farko wanda koda an sa ma ta ciwo idan aka je asibiti da wuri Likitoci za su gane bakin zare a shawo kan lamarin da wuri sannan kuma shi wanda ya yi mata fyaden a hukunta shi dan ya zama darasi ga saura masu irin wannan hali.

Mashawarciyar ta sake yin kira ga yan jarida da suka halarci taron da cewa yana da kyau su ci gaba da yayata wannan manufar ta hanyar labarai da shirye shirye a kafafen yada labarai wanda hakan zai sa kan jama’a ya waye su kuma iyaye za su dai na boyewa idan aka yiwa yarinya fyade sannan kuma mata za su gane boyewar illa ce ga rayuwar Yara kananan da ake yiwa fyade amma idan aka bayyana za’a iya samu a ceto rayuwar su.

Alhassan Yahya Shugaban sashin kula da Yan Jarida na UN Women din wanda kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar yan jarida ta kasa reshen jihar Gombe, kira ya yi ga iyaye kan cewa a lokacin da aka kama wanda ya yiwa yarsu fyade aka kai shi gaban shari’a su dai na zagawa daga baya suna cewa sun janye karar dan gudun cewa ana tonawa yarsu asiri.

Alhassan Yahya, ya kuma ce yana da kyau a samu karuwar mata a bangarorin gwamnati wanda hakan zai sa suna kara bada shawara wajen samar da mafita a wasu bangarorin.

Daga nan sai ya yi kira ga hukumomi da su kara gaimi wajen ganin duk wanda aka kama da sunan fyade a hukunta shi yadda ya dace dan ya zama wa yan baya darasi domin rashin hukunta masu yin fyaden ne yake kara yawaitar laifin a tsakanin al’umma ceto rayuwar su.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: