Iyaye Sun Kadu Da Yankan Ragon Da Aka Yi Wa Dansu Karo Na Biyu A Jos

Daga Hafsat Moh’d Arabi,

A ranar Alhamis 24 ga Satumbar wannan shekara, iyayen wani yaro da ke Unguwar Tudun Pera ta Arewacin Jos, a Jihar Filato, suka tsinci kansu cikin wani yanayi na jimamin rashin dansu, lamarin da ya daga hankalinsu da na makota.

Dan shekara bakwai da rabi a duniya, kuma dan aji daya a makarantar firamare mai suna Abdul’ahad Nasir Bappa, an yi masa ganin karshe a wannan rana ta Alhamis bayan ya dawo daga makaranta, lokacin da aka aike shi da misalin karfe biyu na rana.

Ganin irin yanayin da ake ciki na satar mutane da neman kudin fansa ya sa iyayen Abdul’ahad suka bazama nemansa, sai dai a wannan rana da aka fita nemansa gami da binciken wuraren da ya dace a duba ba a yi dacen ganinsa ba.

Kwatsam washe garin Juma’a da safe a Ungwan Rogo bayan tsagaita saukar ruwan sama mai karfi da aka yi, sai aka tsinci gawarsa an yi masa yankan rago, wanda ke tabbatar da cewa wasu miyagu ne suka yi masa wannan mummunan aiki.

Wata majiyar daga dangin Abdul’ahad ta tabbatar da cewa, ba wannan ne karo na farko da hakan ta faru a kan ‘ya’yansu ba, suka ce hakan ta taba faruwa a shekarar da ta gabata inda aka tsinci gawar wani yaronsu a irin wannan yanayi.

Ana zargin an jefar da gawar Abdul’ahad ne a unguwar ta magudanar ruwa inda ruwa ya dauke zuwa rafin Ungwar Rogo.

A cewar majiyar har yanzu ana cigaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta’addanci.

Da aka tambayi wata ‘yar uwarsa ko ‘yan sanda na da masaniyar abin da ya faru, sai ta ce “Lokacin da abin ya faru bai fi awa biyu da batansa ba ma aka kai rahoto ofishin ‘yan sanda ba su dauki kowane mataki ba, sai bayan da aka ga gawar sannan suka zo dauka za su kai ta asibiti, sannan suke tambaya shin ko akwai wani wanda muke zargi, aka gaya musu babu wanda ake zargi, suka ce shi ke nan babu damuwa za su zo gidan, amma har kawo yanzu (ranar Lahadin da ta gabata) ba su dawo ba kuma babu alamar wani mataki da suka dauka kan lamarin.”

Mun yi kokarin jin ta bakin ‘yan sanda kan lamarin abin bai yiwuwa ba. Amma za mu ci gaba da bibiyar labarin da zarar mun samu karin bayani za mu kawo muku.

 

Exit mobile version