Jadawalin Wakilan Kwamitin Shirya Babban Taron APC Ya Kawo Baraka A Majalisar Dattijai

Nigerian President Muhammadu Buhari (R) speaks to members of the National Assembly after submiting his budget for 2016 in Abuja, on December 22, 2015. Nigerian President Muhammadu Buhari on Tuesday unveiled a 6.08 trillion naira (around $30 billion) budget for 2016, with 30 percent of the estimates allocated for capital projects. / AFP / SUNDAY AGHAEZE (Photo credit should read SUNDAY AGHAEZE/AFP/Getty Images)

Sabon jadawalin  sunayen ‘yan kwamitin shirya babban taron Jma’iyyar APC na kasa ya kawo baraka a Majalisar Dattawa, inda karfin ikon Shugaban Majalisar ya kara tabbatuwa.

Hakan ya biyo bayan kasancewar daya daga cikin Sanatocin da ya yi kaurin suna wajen ja da Shugaban Majalisar, ya zama shine Sakataren kwamitin shirya taron na APC.

LEADERSHIP A YAU, ta kawo labarin cewa Sanata Ben Uwajomogu, (APC Imo ta Arewa), wanda ya zama wakili kuma Sakataren kwamitin shirya taron, yana daya daga cikin Sanatoci 10 da suka kauracewa zaman Majalisar domin nu na rashin amincewar su da dokar da Majalisar ta amince da ita kan yadda za a gudanar da tsarin zabukan 2019, a ranar 14 ga watan Fabrairu 2018.

Daga cikin Sanatocin Majalisar 11 da Jam’iyyar ta APC ta nada a matsayin wakilai cikin kwamitin shirya taron, daya ne kawai cikin su aka sani yana kusa da Shugaban Majalisar, Bukola Saraki, sauran duk ‘yan sai Buhari ne.

Hatta Sanatan da Majalisar ta dakatar da shi kwanan nan, Sanata Obie Omo-Agege, yana cikin wakilan kwamitin.

Sanatocin da ke cikin kwamitin su ne, Ahmed Yerima, Adamu Aliero, Danjuma Goje, Abdullahi Adamu, George Akume, dakataccen Sanata, Obie Omo-Agege, Andrew Uchendu, Abdullahi Danbaba, Baba Kuka da John Enoh.

Wani Sanata wanda bai so mu ambaci sunansa ba ya shaida mana cewa, “Wannan jadawalin sunayen an yi shi ne domin a jefa razani a zukatan Sanatocin APC, a nu na masu cewa, da yawan su zai yi wuya su sake samun tikitin dawowa Majalisar a 2019.

“Hakan zai sa a dauki tsauraran matakai kan Sanatocin da ke nu na ra’ayin rikau din su kan Buhari, nan gaba Sanata Abdullahi Adamu, ne kuma za ka ji matakin da za a dauka a kan sa,  kana iya cewa mayar da martani ne ko ma dai me ka ke iya cewa.

LEADERSHIP A YAU,ta kawo rahoton, Sanatoci, Adamu Abdullahi, Abdullahi Yahaya,  Ibrahim Kurfi, Abu Ibrahim, Abdullahi Gumel, Binta Marshi Garba, Ali Wakil,  Andrew Uchendu, su ne suka bayyana a wurare daban-daban cewa, dokar zaben nan da Majalisar ta yi wa gyaran fuska ranar 14 ga watan Fabrairu 2018, ba za su aminta da ita ba, tunda a cewar su, Shugaba Buhari ne ake son yi wa zagon kasa da ita.

Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka sha zargin sa a Majalisar bisa zargin shirya makarkashiyar tsige Shugaban Majalisar, Bukola Saraki, akwai yiwuwar dakatar da shi daga halartar zaman Majalisar na tsawon sauran kwanukan da suka ragewa Majalisar da zama.

Kwanakin baya ne dai aka tsige Tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa, daga matsayin Shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.

An zarge shi ne da jagorantar wasu Sanatocin shirya makarkashiyar cusa kiyayya tsakanin Sanatocin domin a tsige Bukola Saraki din.

Majalisar ta umurci kwamitin ta na da’a, da ya binciki zargin shirya tawaye a Majalisar wanda ake zargin wasu Sanatoci karkashin jagorancin Sanata Adamu din ke shiryawa.

Makwanni biyu aka baiwa kwamitin ya mika sakamakon binciken na shi domin sanin matakin da ya kamata Majalisar ta dauka.

Matakin da Majalisar ta dauka na bincikar ‘yan Majalisar ya biyo bayan jan hankalin da Sanata Obinna Ogba, ne ya yi kan dokar Majalisar ta 43. Inda ya ce, shaidun da ke tabbatar da ana shirya wannan tawayen su na hannunsa.

“A yau na mike ne da safiyar nan, domin na tona asirin wasu mutane karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu. A watan Janairu, Sanata Isah Hamman Misau, ya yi wata magana a nan, inda ya ke cewa, akwai wata makarkashiyar da ake yi na tsige Sanata Bukola Saraki, da ma sauran shugabannin Majalisar bakidaya.

“To a yanzun haka, ina da kwararan hujjoji a hannu na, da ke nu na wasu mutane na shirya makarkashiyar rikita Majalisar nan, ta hanyar shirya zanga-zanga.

“Ina bukatar a binciki wannan maganan. Ina kuma da hujjojin da zan tabbatar da abin da nake fada. Akwai kalaman da aka yi ta waya tsakanin Sanata Abdullahi Adamu, da wasu mutane.

“Lokacin da maganan nan ta fara fitowa a watan Janairu duk sai muka yi watsi da ita. Ya zama tilas mu dube ta da kyau. Yin watsi da ita ba shine ba. Idan Shugaba ya amince mani, ina son na gabatar da shaidu na cikakku,” in ji Ogba.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Ike Ekweramadu, wanda ya jagoranci zaman Majalisar a ranar, ya amince wa da dan Majalisar ya gabatar da shaidun na shi ga kwamitin Majalisar na da’a domin ya bincike su, ya kuma kawo sakamakon binciken Majalisar cikin makwanni biyu.

A cewar shi, duk wata makarkashiya ta rikita Majalisar, yin gaba ne da mulkin Dimokuradiyya, wanda hakan ba zai yi wa kowa dadi ba.

Idan har an sami Sanata Abdullahi Adamu da laifin da ake zargin sa da shi, za a iya dakatar da shi na wani lokaci mai tsawo, kamar yanda aka dakatar da Sanata Ali Ndume, a shekarar da ta gabata kan yada wasu rahotannin sukan Shugaban Majalisar Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye,  da aka wallafa su a wani shafin yanar gizo.

 

Exit mobile version