Abdullahi Muhammad Sheka" />

Jafaru Ahmed Ya Isar Da Romon Demonkaradiyya Gidajen Yarin Kasar nan –Magaji Ahmad Abdullahi

MAGAJI AHMED ABDULLAHI, Shi ne Kwanturolan Hukumar Gidajen yari, wanda a tattaunarwa da wakilinmu ya yi kokari wajen bayyana irin nasarorin da Shugaban Hukumar na Kasa ya ya yi cikin shekaru biyu da ya yi akan wannan mukami. A tattaunawar da wakilanmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA da NA’IMA ABUBAKAR ya yi dogon bayani kan nasarar da ya samu zuwan sa Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Masu Karatunmu za so su ji tare da wa muke a halin yanzu?

Sunana Magaji Ahmed Abdullahi, kuma a halin yanzu ni ne shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Jihar Kano.

 

Mai Girma Shugaban Kasa ya kuduri aniyar rage cin koson gidajen yarin Kasar nan, Jihar Kano ce Jihar data zarta sauran yawan jama’a, shin ko ya halin gidajen yarin dake karkashin ikonka suke cika a Kano?

Kamar yadda aka sani na smau gidajen yari goma a Jihar Kano wanda babbansu shi ne wanda ke Kurmawa wanda ke dauke da mutane ahalin yanzu guda 2081sai kuma na Goron Dutse wanda ke dauke da mutane 1,550, sai na Wudil mai mutan 600 sauran da suek Sumaila, Rano, T/Wada, Kiru, Gwarzo, Bichi da D/Tofa suna rufe mutane basu wuce 90 ba.

Maganar Cinkoso da ka tambaya shi ne mutanen dake cikin wadanan gidajen yari sun fi karfi adadin da aka gina gidan domin ajiwa, musali Gidan Kurku na Kurmawa an gina shi bisa zaton ajiye mutun 750, amma yanzu akwai sama da mutun dubu biyu acikinsa, haka Goron Dutse anyi shi domin aje mutum 680 amma yanzu suna da sama da 1500. Wannan tasa cinkoso ya zama babban kalubale ga tafiyar da gidajen yari na kasa a yau. Kuma wannan cinkoso na haifar da abubuwa da suka hadar da rashin tsafta, cututtuka g’aikata da kuma daurarru da kuma wuraren koyon sana’a ya yi karanci.

Sannan kuma matsalar cinkoso alokuta da dama kan haifar da matsalar kokarin guduwar wasu daurarrun da kuma fuskantar matsalar tawaye. Saboda haka a louta da dama gudanar da harkokin gidan kan fuskanci matsala da kuma barazana ga jami’an na gidajen yari.

 

Idan Haka ne kasancewar ka guda cikin kwaturololin dake kula da ire iren wadannan gidajen yari a Kasarnan, zuwa yanzu da gwamnatin ta shiga shekaru uku akan karagar mulki, shin ko kwalliya ta fara biyan kuin Sabulu?

Alhamdulillahi zuwan wannan Gwamnatin mai adalci ya taimaka kwarai da gaske, domin Gwamnati ce mai hangen nesa, kasancewar hankalin ta na kan wadanda suke waje da kuma wadanda ke daure. Alhamdulillahi an samu shugabanni masu kaunar kawo sauyi cikin harkokin gidajen yari, wanda suka tsara yadda sai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shiga har cikin gidan Kurkun Kurmawa inda ya ganewa idonsa halin da gidan yarin ke ciki, wannan tasa dole na godewa Gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam, Ministan Harkokin cikin Gida Mai Ritaya Abdurrahaman Bello Danbazau da Shugaban Hukumar gidajen yari na Kasa Alhaji Jafar Ahmad.

Bayan kammala  ziyarar wanna gidan Kurkuke ne da komawar shugaban Kasa, wanda ba’a taba samun wani shugaban kasa da yaek kan karagar mulki databa shiga kurkkuku ya duba halin da daurarru ke ci sai Muhammadu Buhari, komawarsa ked a  ya kafa wani kakkarfan Kwamiti Karkashin  Mai Sharia Ishak Bello, wanda suka aiki ka’in da na’in.

 

Kwanakin Baya Ministan Harkokin Cikin gida ya kaddamar da ginin sabon gidan yari irin na Zamani a Kanowanda a wurin taron an bayyana cewa harda tsarin koyar da sana’u da kuma harkar Noma, me zaka ce dangane da wannan hobbasa na gwamnatin tarayya?

Alhamdulillah kamar yadda na fara ambata maka cewar kafa wancan kwamiti da na ambata ne suka bayar da shawarwarin samar da karin gudajen yari inda aka tsara gina  sabbin gidajen yari guda shida a shiyyoyin kasar nan, kuma kamar yadda aka sani Gwamna Ganduje shi ne gwamnan day a fara bayar da fili tare biyan diyya ga masu gonaki.

An fara aiki gina wannan gidan yari wanda zai dauki mutum 3,000 anan ana aikin a garin  Janugza kuma tuni aiki ya yi nisa domin aiki anci kasha 60%. Tsarin wannan aiki an tanadi Komai akwai dakunan kwana irin na zamani, ga wurare koyar da sana’u, harkar noma sashin kula da lafiya, an tabbatar da cewa idan an gama aikin wannan gidan yari babu wata mai kasa mai irin wannan gidan yari.

 

Ranka ya dade mene dalilin da ke kawo wannan cikoso a gidajen yari ne?

Kamar yadda na fada tunda fari an gina wadannan gidajen yari shekaru aru aru, misali gidana yari farauruwa an gina a shekara  1910 shekaru  108 da suka gabata kuma an gina dashi bisa tsarina je mutane 750, amma yanzu mutane dake cikin gidan yarin Kurmawa sun haura mutun dubu biyu. Saboda haka dole a samu cinkoso, musamman idan akayi la’akari karuwar al’umma sannan kuma jihar Kano jiha cibiyar Kasuwanci wadda ke karbar baki daga ina hakan yasa dole a samu yawaitar masu aikata laifuka iri daban daban.

 

Wasu na ganin da zarar an ambaci gidan yari ana nufin wani wurin kunci ne, shin  ranka ya dade kila jama’a zaso jin abinda ake nufi da gidan yari?

Gaskiya ne jama’a sun yiwa Kalmar gidan yari mumuunar fahimta domin wuri ne nagyaran halayya, kasancewar da yawa ma zauna wannan gida wasu kaddara ceta kai su, don haka wuri ne da ake kokarin saita halayyar wanda ya tsinci kansa acikin gidan tare da fatan idan ya koma cikin jama’a ya zama nagartacce.

Don haka wanda ke cikin wannan gida ya canci abashi abinci, lura da Lafiyarsa, yana da hakkin samun damar ziyartarsa, shi gidan yari yana matsayin rariyar tace halayyar al’umma ne. Babban kalubalen da ke damun mu shi ne yadda  bayan tace halayyar  mai laifi, amma bayan fitarsa daga djarun sai ya zama abin kyama atsaknin al’umma, Lallai muna kira ga al’umma adaina kyamar wanda ya fita daga gidan yari., domin da yawa kaddara ce ta kaisu wadda kuma ba wanda ya wuce ta same shi.

 

Wanda duk ya sha inuwar gemu ba kamar makogoro ba, shin ya kake ganin irin gudunmawar shugaban Hukumar gidajen yarin Kasar Alhaji Jafaru  Ahmad?

Kamar yadda na ambata duk inda ka hangi nasara babu shakka an samu jajirtaccen jagora, Alhaji Jafaru Ahmad sanin kowa ne  gogaggen ma’aikaci ne hakan ta sa a shekara biyu da zuwansa wannan hukuma, bayan ya yiwa  harkokin hukumar kallon tsanaki ne ya fara da aiki gyaran tarbiyar ma’aikata, tabbtaar da gaskiya da rokon amana.

Hazalika wannan jagora namu ya tabbatar da bayar da Gudunmwarsa ga ma’aikata, musamman batun  ciyar ma’aikata sama da dubu  20,000, kafin zuwansa akwai masu shekara 15 ba tare da samun karin girma ba. Ni kai na ina matsayin mukaddshin kwantarola tsawon shekara goma sha daya, sai da Allah ya kawo shi sanan na motsa zuwa Kwantirola.Haka kuma  kwanan nan za’a kara fitar da wani Jerin  sunayen wadanda ake sa ran ciyarwa gaba,

Cikin tagomashin da hukumar gidan yari ta samu zuwan wannan bawan Allah ya tabbatar inganata harkar tsafata tsakanin ma’aikata ta fuskar samar da uniform saiti biyu ga dukwa wanj Jami’in gidan yari dake kasarnan, Sannan kuma Ja’afar Ahmad ya gwangwaje dukkan manyan jami’an wanna hukuma da Motocin aiki sabbi ga ma’aikata,

 

Haka kuma bangaren harkar noma ya samar da motoacin noma a ofisoshin dake fadin karasarnan a hukumar lura da gidajen yari, ni shaida an kuma samar da moticin ambulas da motocin daukar ruwa.  Zamninsa aka samu karin kudin ciyarwa a gidaje yari, inda ake bayar abinci mai gina jiki.

A bangaren lafiya saida ya tabbatar da ganin an samar da maganunuwa a gidaje a lokacinsa na biliyoyin naira.Saboda ina tabbatar maka da cewa a lokacinsa ne ainihin romondemokaradiyya ya isa gidajen yarin Kasarnan.

 

Ya danganta ka take tsakanin ka da Jami’an wannan Hukuma tunwanka Kano?

Alhamdulillahi Koyi muke da jagoranmu na kasa, shi ma’aikaci na son ka kyautata masa, saboda haka tun zuwa na Jihar Kano abinda na mayar da hankali kenan wajen tabbatar da kyakkyawar danganta tsaknina da abokan aikina, duk wani hakki nasu na kanyi bakin kokari wajen ganin sun same shi, kuma alhadulillahi ido ba mudu ya sasan kima, ina samun hadin kan abokan aiki na yadda ya kamata

 

Mene sakonka ga al’ummar Kano, musamman kan abinda ya shafi batun gidajen yari?

Sakona bag a Jama’ar Kano kadai ba harma kasa baki daya shi ne jama’a su fahici mu hidimace muek yiwa al’umma, da yawa mutane har yanzu basa san muhimmacin gidanyari ba, mune tsaron baki daya, don haka mu rumbune na bayanai don haka wannan aiki ne mai muhimmanci ga kowa, kamar yadda aka sani shi gadan yari tunda Allah ya yi halitta yana nan a tsarin  wanda duk y aaikata laifi aje a hukunta shi. Kiran d azan yi kenan jama’a su fahimci ayyukan gidjjen yari aiki ne na tsaftace al’umma mu matsayin rariya muke, wannan shi ne kira na ga jama’a.

 

Exit mobile version