Daga Mustapha Ibrahim,
Jagoran siyasar Karamar Hukumar Bunkure, Dakta Yahaya Isah Bunkure, da sauran shugabanin masu taimaka masa jan ragamar Karamar Hukumar Bunkure da ke Jihar Kano a siyasance, sun yaba wa Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kan kishinsa na ciyar da Kano gaba ta kowace fuska kamar dai yadda suka bayyana a zantawarsu da manema labarai a garin Bunkure karkashin jagorancin siyasar Bunkure. Dakta Yahaya Isah Bunkure kuma shugaban Kwalejin Horar da Malaman makaranta ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a Kano.
Tun da farko a Jawabinsa Dakta Yahaya Isah Bunkure wanda kuma shi ne Makamann masarautar Rano, ya bayyana cewa irin tsarin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zo da shi na Ilimi kyauta abu ne da ya da ce da wannan yanayi na bukatar bunkasa ilimi da kuma tallafawa alumma, ga kuma tsarin bunkasa makarantu da gine-gine wanda makarantar Sa
adatu Rimi ba ta taba samun cigaba ba kamar zamanin Ganduje ba.
Sannan shi ne gwamna na daya wajen ware kashi 25 da digo 32 a kasafin kudi don cigaban Ilimi wanda babu wani gwamna a Nijeriya da ya yi wannan kokari sai shi.
Ita kuwa kallabi a tsakani Rawuna Hon Dakta Mariya Mahmud Bunkure Kwanishiniyar ta ce an samu nassara a zaban kananan hukomomi na Kano kamar yadda ta kamamata inda suka sami kananan hukomumi da Kansaloli Kano baki daya.
Bugu da kari Dakta Mariya wacce ta samu rakiyar wakilin Gwamna Kano Honarabul Auwalu Ubale Minjibir da sauran jami’an Gwamnatin Kano irinsu Dakta Habibu Liman Kafamai, daya daga cikin mashawarta ga Gwamnatin Kano, haka kuma ciki tawagar akwai irinsu Honarabul Umar Mai shinkafa wanda aka fi sani da Umar Mai Rice wanda shi ma na daga cikin masu taimakawa kan harkar hada labarai da suka raka Dakta Mariya ta yaba wa jama`ar Bunkure kan yadda suka fito a lokacin zabe, da kuma yadda suke ba Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje Hadin kai.
A na sa bangaran shugaban Jamiyar APC a Karamar Hukumar Bunkure Honarabul Rabiu Haliru Gurjiya ya ce duk wata nasara da ake samu a siyasance, ta samu asali ne daga jagororin wannan yanki na Kano ta Kudu irinsu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, sai Honarabul Kabiru Al
hassan Rurum da kuma Honarabul Muhammad Maishanu, irinsu Dakta Yahaya Isah Bunkure da dai sauran shugabanin wannan shiyya a Kano ta Kudu.
Shi ma Honanarabul Rabiu Bala Bunkure Shugaban Karamar Hukumar, mai barin gado ya ce mulkinsa na shekara shida ya kawo gagarimun sauyi na cigaba a karamar hukumar Bunkure, kamar samar da ofishin ‘yan sanda a garin, babban Masallaci, Makarantu masu yawa da kuma samar da babbar Makaranta ta Gwamnatin Tarayya a Bunkure, sakamakon shige da fice da ya yi na samun aikin daga sama, baya ga gina babban Asibiti, samar da magudanan ruwa, da dai sauran ayyuka da titi a cikin garin Bunkure da kewayanta sakamakon hadin kan da ya samu daga Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma ya yi fatan sabon shugaban karamar hukumar Bunkure zai dora a kai kasancewarsa mataimaki a hawa biyu da suka yi da shi.
Shi ma a nasa jawabin, sabon mataimakin shugaban Karamar Hukumar, Honarabul Abba Kawu Gurjiyaya ce baban burinsa shi ne ciyar da jamaar Bunkure gaba a wannan lokaci, kuma yana ganin babu wata nasara da zai samu ba tare da jama
ar Bunkure sun samu cigaba ba, don haka suna neman addua da shawarwarin al
umma a wannan mulki da zaa tallafawa al
umma kamar yadda ta kamata.
Shi dai Honnarabul Abba Kawu Gurjiya, ya yi karatunsa na Firamare ne a garin Gurjiya, ya yi Sakandiransa a Kibiya, sai ya wuce zuwa, Makarantar Ligal da ke kano inda a nan ya yi Diploma, sannan karatun HND a makarantar kimiyya da fasaha ta Kano wato ‘Kano State Polytechnic’ kuma shi da ne ga fItaccen dan siyasar nan na Kano Marigayi Honarabaul Alhaji kawu Gurjiya.
Haka kuma wakilimu da ya kasance a KANSIEC ya rawaito mana cewa, Jam`iyar APC ta samu kuri’u milliyan 2.357 wanda ya bata nasarar cinye zaben shugabanin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 na Jihar Kano kamar dai yadda Farfesa Garba Ibrahim Sheks, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta KANSIEC, ya bayyana ga manema labarai a ofishinsa bayan kammala zaben na ranar Asabar 16 ga watan Janairu 2021.