Nasiru Adam" />

Jagorancin Sarkin Zazzau Abin Koyi Ne–Inji dan Dukajin Zazzau

A cikin karshen makon da muke ciki ne a lokacin bukukuwan cika shekaru 45 da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji (Dkt) Shehu Idris ya yi akan karagar mulki ,wakilin mu ya sami zantawa da daya daga cikin yayan manyan sarakunan Zazzau watau dan sarkin Dukajin Zazzau Shehu Adamu Garba, a bisa irin nasa hasashen da nasarorin da mai martaban ya samu a cikin wannan shekarun.Ga kuma yadda hirar tasu ta kasance .
Ranka ya dade da yake kana daya daga cikin manyan yayan Sarakuna a wannan masarautan ta Zazzau, kuma ga shi a yaune mai martaba Sarkin zazzau ke cika shekaru 45 ko me zaka baiyyanawa masu karatun mu?
Auzu billahi minashaidani rajim Bismillahi rahmani rahim, agaskiya a wannan lokacin ina mai matukar farin ciki wanda baya misaltuwa , domin kuwa Allah ya nuna mini wannan rana da uban mu mai Martaba Sarkin Zazzau ke cika shekaru 45 da biyar a bisa karagar mulki , wanda tunkafin a haife ni da ire-irena masu kanannan shekaru yake wannan sarauta, sai gashi ana taya shi wannan murnan tare da ni .
Yazuwa yau ko me zaka fadawa masu karatunmu ,irin nasarorin da aka samu a cikin wadannan shekaru masu albarka?
To Alhamdu lillahi, wannan tambayar da kayi mini tambaya ce ma fadin gaske , domin duk wanda zai bada amsarta bazai iya kewayeta da cikakkiyar amsar ta ba, saidai ya yi maka dan tsokaci kadan a kan abin da ya sani nima bai wuce in tsakuro maka kadan daga ciki ba. Misali ga yan kadan daga ciki irin nasarorin da nasan cewar sakamakon kyawawan jagorancin mai Martaba ne aka same su.misali2 zaman lafiya da ppppfahimtar juna a tsakankani kabilu da kuma banbance banbance Addini da suke da shi amman wannan bai hana su zaman lafiya baa.
Me za ka ce dangane da batun illmi a kasar zazzau.
To ai da ma can sanin kowa ne kasar zazzau ta ciri tutar yabo a kasarnan a fagen ilimi, don haka duk wata cibiya ta ilimi da ke kasar zazzau akwai sa hannun mai maraba a cikin ta kafin ta zamto a yaddza take a halin yanzu
Daga karshe wane fata kake yi wa mai martaba a bisa wannan jagorancin da yake yi?
To babban fata na bai wuce fatan alkairi da tsawaicin kwana tare da ci gaban jagorancin da yake yi mana, kuma Allah ya kara hada kan al´ummar kasar zazzau tare da fahimtar juna.

Exit mobile version