Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin ya ce jagororin hukumomin tsaro, da na rundunonin sojoji daga sama da kasashe 100, za su halarci taro na 12 na dandalin Xiangshan a birnin Beijing.
Jami’in da ya bayyana hakan a Larabar nan, ya ce cikin kasashen da suka bayyana aniyar turo manyan wakilan, akwai Vietnam, da Singapore, da Rasha, da Faransa, da Najeriya da Brazil. Ya ce taron dandalin na Xiangshan, zai gudana ne a tsakiyar watan nan na Satumba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)