Jakadan kasar Sin: Matan Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa A Cikin Al’umma

Daga CRI Hausa

Yayin da ake bikin ranar mata ta duniya a jiya, zaunannen jakadan kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyanawa duniya cewa, matan kasar na taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma.
Ya ce yayin da ake tunkarar annobar COVID-19, mata ne a kan gaba wajen yakar cutar. Ya ce sama da jami’an lafiya 40,000 daga fadin kasar Sin ne suka garzaya lardin Hubei a lokacin da cutar ta barke, kuma 2 bisa 3 na adadin, mata ne.
Ya ce a fannin yaki da talauci, ba gajiya kadai mata suka ci ba, domin sun kasance masu bada gudunmuwa. Yana mai cewa, mata ne suka mamaye kimanin rabin mutanen karkara da suka fita daga kangin talauci. Kana 5 daga cikin mutane 10 da aka karrama a matsayin abun koyi a fannin yaki da talauci, mata ne.
Da yake jawabi game da zaman lafiya, jakadan ya ce sama da matan Sinawa 1,000 ne suka yi aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Sudan ta Kudu da Mali da Haiti da sauransu.
Bugu da kari, ya ce mata na taka muhimmiyar rawa a fagen siyasar kasar Sin. kuma suna farin ciki da ganin wakilai mata daga dukkan kabilu, a majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da majalisar tuntuba kan harkokin siaysa. (Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version