Majalisar dattijai, a yau Talata, ta tabbatar da nadin tsoffin shugabannin hafsoshin rundunar tsaro a matsayin jakadu na musamman.
Wadanda aka zaba din su ne: Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya) (Ekiti); Lt-Janar. Tukur Buratai (mai ritaya) (Borno); Admiral Ibok- Ette Ibas (mai ritaya) (Cross River); Air Vice Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) (Bauchi); da Air Vice Marshal Muhammad S. Usman (Rtd) (Kano).
Tabbacin nasu ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar dattijai kan harkokin kasashen waje, karkashin jagorancin Sanata Adamu Bulkachuwa (APC, Bauchi).
Akwai Wani yunkuri da Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi, na jawo hankalin takwarorinsa game da neman kin tabbatar dasu, amma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya tsayar dashi.
Abaribe ya nemi Bulkachuwa da ya yi bayanin dalilin da ya sa aka dakatar dashi kan korafin sa amma Lawan ya ce karar ba ta da wani amfani.