Daga CRI Hausa
A watan Fabrairu na bana, tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Equatorial Guinea, sun isa birnin Malabo, fadar mulkin kasar, lamarin da ya sa, kasar Equatorial Guinea ta kasance kasar dake nahiyar Afirka ta farko, da ta samun tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 daga kasar Sin.
Bayan aka yi masa allurar, shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya ce, allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samarwa sun ceci rayuwar al’ummomin nahiyar Afirka.
A nata bangare kuma, jakadar kasar Sin dake kasar Equatorial Guinea Qi Mei ta bayyana cewa, hadin gwiwa a fannin allurar rigakafi ta bai wa kasar Equatorial Guinea goyon baya wajen cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, ta kuma kasance sabuwar damar karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin kiwon lafiya da dai sauransu.
Jakada Qi ta kara da cewa, a ranar 10 ga watan Fabrairu ne, tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta baiwa kasar Equatorial Guinea suka isa birnin Malabo, kuma mataimakin shugaban kasa da ministoci da dama, sun tarbi jiragen saman dake dauke da rigakafin da kansu, domin maraba da zuwan alluran rigakafin cutar ta COVID-19. An kuma yi bikin mika alluran rigakafi a filin jirgin saman kasar. Kaza lika, an fara yin amfani da allurar cikin kasar Equatorial Guinea a hukumance. A halin yanzu kuma, ana yi wa al’ummomin kasar allurar bisa jadawalin da aka tsara. Tana mai cewa, “An baiwa kasar Equatorial Guinea tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19, domin cika alkawarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, game da karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama a fannin kiwon lafiya, da kuma alkawarin da ya yi, cewar za a baiwa kasashen Afirka tallafin alluran rigakafi da farko, bayan kasar Sin ta gama aikin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19. Wannan shi ne karo na farko da aka mika tallafin alluran zuwa wata kasar Afirka, kuma, an fara yin rigakafin ga al’ummomin kasar Equatorial Guinea nan take.
Abu mafi jan hankali a nan shi ne, an yi wa shugaban kasar Equatorial Guinea allura a ranar 11 ga watan Fabrairu, wato rana ta biyu bayan aka kai allurar kasarsa. Sa’an nan, an kuma yi wa likitoci, da ma’aikata masu bukatar samun allurar wannan rigakafi cikin gaggawa. A halin yanzu kuma, ana ci gaba da aiwatar da aikin samar da alluran rigakafi ga al’ummomin kasar bisa jadawalin da aka tsara. Kuma bisa labaran da kafofin watsa labaran kasar Equatorial Guinea suka samar, an riga an yi wa ’yan kasar Equatorial Guinea dubai allurar ta farko. Wasu kuma, an riga an yi musu allurar ta biyu. Muna iya cewa, an fara yi wa kaso 4% na al’ummun dake birnin Malabo wannan allura.”
Ta kuma kara da cewa, an riga an yi wa jami’an kasar Equatorial Guinea da yawa allurar rigakafin da kasar Sin ta samar, dukkansu sun nuna yabo matuka kan ingancin allurar, sun jinjinawa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Jakada Qi Mei ta ce, “Bayan aka yi masa allura, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya ce, allurar rigakafin da kasar Sin ta samar ita ce mafi inganci. Kasar Sin ta ceci rayukan al’ummomin kasashen Afirka, ta hanyar samar musu alluran rigakafin cutar COVID-19. Hari la yau, kasar Sin abokiyar arziki ce ta kasarsa, kuma ‘yar uwa ce ga dukkanin kasashen Afirka. Mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Nguema Obiang Mangue, shi ne mutumin farko da aka yi masa allurar rigakafi a kasar. Ya kuma ce, allurar rigakafin kasar Sin tana da inganci, an masa allurar da farko, domin ya zama abin koyi ga al’ummomin kasarsa. Haka kuma, bayan da aka yi musu alluran rigakafin da farko, wasu masu aikin likitanci sun ce, suna farin ciki matuka game da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasarsu da kasar Sin, da kuma yadda suka samun tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 daga kasar Sin. Sun kara da cewa, ba su gamu da matsala ko kadan ba, bayan aka yi musu alluran. Alluran rigakafin da kasar Sin ta sarrafa suna da inganci sosai, shi ya sa, suke kira ga al’ummomin kasar da su samu alluran rigakafin cikin sauri.”
Jakada Qi ta ce, bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin da kasar Equatorial Guinea, sun ba da taimako da goyon baya ga juna. Yadda suke yin hadin gwiwa wajen yaki da annobar, ya nuna kyakkyawan zumunci da fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu. Tana mai cewa, “A shekarar 2020 da ta gabata, gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta samar wa kasar Sin taimakon kudi har dallar Amurka miliyan 2, domin goyon bayan kasar Sin wajen yaki da annoba. Kasar Sin ta kuma samar wa kasar Equatorial Guinea kayayyakin yaki da cutar sau da dama, yayin da kuma ta tura likitocin yaki da cutar zuwa kasar Equatorial Guinea, domin samar mata taimako ga masu bukata. A bana kuma, hadin gwiwar kasashen biyu a fannin allurar rigakafin cutar COVID-19, ta samar da goyon baya mai karfi ga kasar Equatorial Guinea, wajen cimma nasarar yaki da cutar baki daya, wadda ta kasance sabuwar damar karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fannin kiwon lafiya da sauransu.
Ma iya cewa, hadin gwiwar Sin da Equatorial Guinea a fannin allurar rigakafi, ya nuna bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)