Jakadun Afirka Sun Kai Ziyara Jihar Xinjiang Ta Sin

Daga CRI Hausa

A ranar 26 ga wata, jakadu da jami’an diflomasiyya daga kasashen Afirka 30, da suka hada da kasashen Kamaru, Benin, Burundi, Saliyo, Somaliya, Burkina Faso, da kasar Mauritius da sauransu, da kuma wasu wakilan kungiyar tarayyar Afirka AU sun kai ziyara a jihar Xinjiang ta kasar Sin bisa gayyatar da aka yi musu, domin su ganewa idanunsu ci gaban da aka samu a jihar a fannin bunkasuwar tattalin arziki, da kyautatuwar rayuwar al’ummomin jihar.

Bayan da suka isa birnin Urumqi a ranar 26 ga wata, sun kai ziyara a wajen bikin nune-nunen ayyukan yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi da aka yi a jihar Xinjiang, inda suka kara fahimtarsu game da mawuyacin halin da ake ciki a lokacin da aka dukufa wajen yaki da ta’addanci a jihar, sun kuma nuna amincewarsu kan matakan da Sin ta dauka wajen yaki da ta’addanci da kawar da masu tsattsauran ra’ayi a jihar Xinjiang.

A babban masallaci mai suna White Mosque dake birnin Urumqi, wakilai sun yi hira da Liman, domin kara saninsu game da yadda ake gudanar da harkokin addini a jihar, sun kuma gamsu matuka kan yadda ake kiyaye ‘yancin al’ummomin jihar Xinjiang a fannin bin addini.

Haka kuma, wakilai sun kai ziyara a babbar kasuwar Bazaar ta kasa da kasa ta jihar Xinjiang, sun nuna sha’awarsu matuka game da al’adu na musamman na jihar Xinjiang, sun kuma nuna yabo matuka ga gwamnatin kasar Sin dangane da kokarin da ta yi wajen kiyayewa da kuma yada al’adun kabilu daban daban na jihar Xinjiang.

Jakadan kasar Benin dake kasar Sin Simon Pierre Adovelande ya ce, bayan ziyararsa a babbar kasuwar Bazaar, yadda ake raya tattalin arzikin jihar Xinjiang cikin himma da kwazo ya burge shi kwarai da gaske. Kuma, yana fatan kara saninsa game da harkokin jihar Xinjiang, domin habaka hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakanin bangarorin biyu a fannin raya tattalin arziki da al’adu da sauransu. (Mai Fassarasa: Maryam Yang)

 

Exit mobile version