CRI Hausa">

Jakadun Kasashen Waje Dake Sin Sun Nazarci Nasarar Da Kasar Ta Samu A Yaki Da Talauci

Yayin da kasar Sin ke gudanar da ranar yaki da talauci karo na 7, wanda ya fado rana guda da na MDD, sama da wakilai 400 na jam’iyyun siyasa da jakadun dake kasar Sin da masana daga kasashe sama da 100 ne suka halarci taron karawa juna sani kan dabarun yaki da talauci da hakkokin dake wuyan jam’iyyun siyasa, wanda ya gudana ta kafar intanet a lardin Fujian na Sin.

Jakadun sun bayyana cewa, nasarar da Sin ta samu wajen yaki da talauci sun samar da darasi ga daukacin duniya, kuma suna fatan kara hadin gwiwa da Sin.
Yaki da talauci da inganta zaman takewar al’umma daya ne daga cikin manyan kalubalen da duniya ke fuskanta. A fannin yaki da talauci, dabaru da matakai da hikimar kasar Sin sun samar da darussa ga sauran sassan duniya.
A cewar Mohammed Elbadri, jakadan Masar a kasar Sin, koyi da kasar Sin a fannin yaki da talauci, abu ne mai matukar amfani, wanda kuma ya kasance muhimmin aiki da ke gaban jakadun kasashen waje.
Shi kuwa jakadan Pakistan a kasar Sin, Moin-ul-Haque cewa ya yi, nasarar kasar Sin abun koyi ne, inda ya ce, talauci babban kalubale ne ga dukkan bil adama, kuma akwai dubban mutane dake rayuwa cikinsa a kasashe da dama, don haka, dole ne kasashe su sanya batun yaki da talauci a kan gaba cikin manufofinsu. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version