Nasir S Gwangwazo" />

Jama’a, A Zauna Lafiya Bayan Zabe

Zabe wani abu ne wanda ya ke zuwa ya gudana tsakanin mutane biyu ko fiye da haka, amma guda daya ne kacal zai lashe zaben a tsakanin wadanda su ka yi takarar. Hakan ya na nufin cewa, saura za su hakura kenan duk irin juyin da a ka yi, yayin da guda daya zai dare kan kujerar.
Wannan faduwa a zaben da sauran ’yan takarar su ka yi ba ya nufin cewa, ba su da farin jini ko kuma ba su isa su hau kan kujerar ba ne, illa dai kawai dole ne sai mutum daya ne zai hau kuma kowane dan adam ba ya wuce irin tasa kaddarar.
Don haka babu dalilin tayar da kayar baya matukar mutum ya yarda da kaddara mai kyau da maras kyau. Hakan nan kuma kai ma ba za ka so a ranar da Allah ya ba ka taka nasarar ba a tayar ma ka da kayar baya ko a zubar da jini ba.
Sau da yawa masu tayar da kayar baya a lokacin zabe, za ka tarar cewa, ba su ne ainihin ’yan takarar ba, domin dan takara ba dan yaga-riga ba ne kuma ya san ya na da makomar da watarana zai iya sake tsaya wa takara ya kuma ci zaben. Don haka ba zai iya fitowa da kansa ya shiga jerin masu tayar da kayar baya ba. Ba shi ba ma, hatta ’ya’yansa na cikinsa ba za su yi hakan ba, domin su ma iyayensu su na yi mu su tanadin kyakkyawar makoma ba ta yaga-riga ba.
Wannan batu na matasan da a ke yin amfani da su ne a tayar da rikici bayan zabe, saboda an haramta mu su ingantaccen ilimin da za su fahimci irin cutarwar da masu zuga su su ke yi har sai an yi mu su bayani.
Bugu da kari, a irin wannan lokaci da jami’an tsaro su ka tashi tsaye, sannan gwamnati ta ke zare idanu kan bin doka, zai yi wahala idan an kama mutum a sake shi cikin sauki, domin doka za ta iya yin aiki a kan kowa; ciki kuwa har da wanda ya ke daukar nauyin ku matasan da ku ke tayar da kayar bayan.
A karbi kaddara a tari gaba zai fi zama alheri, domin a lokuta da dama ka kan so abu tsananin so, amma ya zama sharri a gare ka. Haka nan ka kan ki abu tsananin ki, amma ya zama shi ne mafi alheri a gare ka. Wannan lafazi ne na Ubangiji.
Saboda haka mu na masu jan hankalin matasa da iyayen gidansu a kan su ji tsoron Allah su kiyayi haifar da tunzuri bayan sanar da sakamakon zabe. Duk rikicin da ya tashi, zai iya zuwaya dawo kansu, domin idan dan adam ya san farkon fitina, to fa bai san karshenta ba. Ba za ka taba gano ta hanyar da fitinar za ta dawo kanka ba, sai a lokacin da ta zo kan naka.
Allah Ubangiji ya kiyashe mu, sannan ya nufe da wanyewa lafiya a wannan lokaci mai sarkakiya da kuma bayansa, amin summa amin.

Exit mobile version