Jama’a Ayi Hattara!

Fashi da warcen wayoyi ya na kara ta’azzara a cikin garin Abuja, a watan da ya gabata akan hanyar Kubwa wata mata ta na zaune a gaban mota su na tafiya a cikin mota wani mutum da ba a san ko wayewa ba ya fito da gudu ya warce wayarta ya fada cikin daji da gudu. Haka a cikin watan da ya gabata motar haya dauke da fasinjoji daga Minna su na shigowa aAbuja wasu mutane su ka tare  su, su ka lalube kowa su ka kwashe wayoyinsu da kudadensu.

Sati biyu da ya  gabata, akan hanyar Gwarumpa life camp by -pass da misalin karfe takwas da minti goma sha biyar na dare miji da matarsa su na tafiya a cikin mota wasu mutane suka datse musu hanya su ka kkwace musu wayoyi masu tsada da kudadensu.

A cikin satin nan akan gadar kado-life camp da misalin karfe takwas na dare, wani Alhaji tare da yaronsa su na tafiya sai motar ta fara cijewa ta ki tafiya, tsayawar da su ka yi kenan don su duba wasu mutane su ka firfito su ka yi kamar za su taimake su sai kawai su ka dora musu wokake a wuya su ka lalube musu aljifai su ka kwashe kudadensu kakaf da wayoyinsu masu tsada har da lab top. Su ka kwace mukullin motar da zummar za su gudu da maotar sai ba ta tashi ba, da su ka mutane sun fara tsayawa sai su ka diddira kasan gada su ka gudu.

Ire-iren wadannan abubuwa su na ta faruwa a wurare daban-daban a cikin kasar nan gaba daya, a garin kano kuwa wata dalibar jami’a ce ta taso daga lacca ta na bayan adaidaita sahu,ta na amsa waya wasu mutane maza guda biyu akan babur su  ka matso dab da ita na bayan ya sa ka hannu ya fisge wayar ta mai tsada da rana tsaka ana kallonsu, babu abin da aka iya yi su ka gudu.

 

Da fatan wadanda abin ya shafa za su dauki mataki don kare lafiya da dukiyar al’umma. Jama’a ku ma su kiyaye bin hanyar da babu kowa da kuma fitar da wayoyinsu a kan hanya saboda ma su warce. Allah Ya dada kiyaye mu.

 

Exit mobile version