Connect with us

LABARAI

Jama’a Na Kokawa Saboda Daga Gobe Farashin Lantarki Zai Rubanya

Published

on

Masu amfani da hasken lantarki a Nijeriya su na ta faman kokawa a bisa karin da aka yi wa kudin lantarkin wanda zai ribanya abinda a ka saba biya a baya daga gobe Laraba, 1 ga Yuli, 2020.

Ministan samar da hasken lantarki, Sale Mamman, tun a ranar 15 ga watan Yuni ne ya shelanta cewa ‘yan Nijeriya za su biya karin kudin hasken lantarki da su ke zuka tun daga ranar 1 ga watan Yuli.

Sale Mamman ya shaida wa kwamitin majalisar Dattawa cewa, “Ba mu da wani zabi matukar mu na fatan warware matsalar samar da hasken lantarki a kasar nan face mu yi karin kudin.”

Ya shaida wa kwamitin majalisar Dattijai kan hasken lantarki cewa, karin kudin hasken lantarkin shi ne kadai hanyar warware matsalar sashen lantarkin a kasar nan.

Sai dai kuma a jiya da dare kamfanonin da su ke aikin rarraba hasken lantarkin sun yi gargadin cewa yin karin kudin lantarkin ba fa zai kara yawan hasken lantarkin da ake samu ba a yanzun haka.

Kamfanonin a karkashin kungiyarsu ta masu rarraba hasken lantarki ta, Association of Nigerian Electricity Distributors (ANED), ta ce sabon farashin hasken lantarkin fa ba zai zo ne da wani siddabaru ba da zai sanya a sami hasken lantarkin a kowane lokaci.

Babban daraktan kungiyar ta ANED, Sunday Oduntan, ya shaida wa wakilinmu a tattaunawar da suka yi da shi a daren jiya ta waya cewa, “Za a sami canji in an kwatanta da shekaru biyar a baya, sai dai kuma ka da fa a sa ran cewa za a rika samun hasken lantarkin ne na tsawon awanni 24 a kullum.

Ya kara da cewa, “Matukar dai akwai mutanan da su ke ci gaba da shan hasken lantarkin ba tare da mita ba, matukar akwai ma’aikatan lantarkin da su ke yin cuwa-cuwa a aikin na su, sannan matukar akwai ‘yan Nijeriyan da ba su shirya su rika biyan kudin lantarkin da suka zuka ba, to kuwa za a ci gaba da samun matsala a bangaren na hasken lantarki.

Ya ce: “Kamfanonin rarraba hasken lantarkin sun koka a kan yin karin kudin lantarkin, hukumar samar da hasken lantarkin ta NERC ba za ta iya nisanta kanta da karin kudin lantarkin da aka yi niyyan yi ba daga ranar 1 ga watan Yuli.

“Sai dai abin da ke faruwa a cikin ‘yan kwanakin nan shi ne, kamfanin samar da hasken lantarkin yana ta gargadinmu da ka da mu ambato sunansa ko na gwamnatin tarayya a kan karin kudin lantarkin ga al’umma, wanda sam hakan mu ba a yi mana adalci ba.

“Mu na son ‘yan Nijeriya su san cewa yin karin kudin hasken lantarki ko yin ragi sam ba mu ne ke da hakkin yin sa ba, hukumar ta NERC ce ke da wannan hakkin a matsayinsu na masu samar da hasken lantarkin. Mu namu shi ne mu bayar da shawara kadai amma su ne ke da yanke hukunci.

“Mun yi mamakin samun sako na musamman daga hukumar ta NERC wacce ta rarraba wa dukkanin kamfanonin rarraba hasken lantarkin tana gargadinmu da ka da mu kuskura mu ambaci sunansu ko na gwamnatin tarayya a kan karin hasken lantarkin.

A gab da yin karin kudin lantarkin, kungiyoyin masu amfani da hasken lantarkin a karkashin kungiyarsu ta, Organised Pribate Sector in Nigeria (OPSN), sun ce duk wani karin da za a yi a kan kudin lantarki a kasar nan matukar dai ba ana iya samar da wadatacciya kuma ingantaccen hasken lantarkin ne ba, hakan zai kara tsadar farashin kayayyakin bukatu ne kawai a kasar nan, sannan kuma hakan zai haifar da rasa ayyukan yi.

kungiyar ta OPSN ta kunshi kungiyoyin masu sarrafa kayayyaki ta, Manufacturers Association of Nigeria (MAN), kungiyar ‘yan kasuwa da masu masana’antu ta, Nigerian Association of Chambers of Commerce, Industry, Mines and Agriculture (NACCIMA), kungiyar tuntuba ta masu daukan ma’aikata ta, Nigeria Employers Consultatibe Association (NECA), kungiyar masu kanana da matsakaitan kamfanoni ta kasa ta, Nigerian Association of Small and Medium Enterprises (NASME) da kungiyar masu kanana da matsakaitan kamfanoni ta kasa ta, the Nigerian Association of Small Scale Industrialists (NASSI).

Babban daraktan kungiyar ‘yan kasuwa da masu masana’antu ta Jihar Legos, Dakta Muda Yusuf, ya ce shirin farfado da sahen lantarki na kasar nan sam bai haifar da da mai ido ba.

Ya ce akwai bukatar tunkarar shirin ne yanda ya kamata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: