Connect with us

JAKAR MAGORI

Jama’a Sun Kawar Da Shingen ’Yan Sanda Yayin Zanga-zangar Katsina

Published

on

Dandazon jama’a a Jihar Katsina sun fito domin yin zanga-zanga a kan hauhawan rashin tsaro a fadin jihar. Masu zanga-zangar sun kawar da shingen da jami’an ‘yan sanda suka sanya a manyan tituna yayin gudanar da tattakin nasu, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

A wani sakon murya da majiyar mu ta samu, an jiyo daya daga cikin jagororin zanga-zangar mai suna Kwamred Usman Hussaini Rafuka yana fadin cewa: “Musababbin wannan zanga-zangar da muka shirya, kowa dai ya sani musamman indai mutum yana a yankin Arewacin Nijeriya, ya san menene musababbin. “Musababbinta bai wuce yanayin yadda ake kisan al’umma, musamman idan kika dauki Jihar Katsina, muna da Kananan Hukumomi kusan 15 wanda a kullum sai an zub da jini a wannan yankin.

“Da wuya ka ji an ce ba a kashe mutum 20 ba kai har mutum 100 ana kashewa a rana daya.

“Yanzu haka maganar da nake yi da safe akwai wanda yana daga cikin masu wannan zanga-zangar lumanan da muka shirya, wanda da safen nan na kira shi ya batun tafiya sai yake ce mun wallahi yanzu haka a jiya a Batsari akwai wani gari an shiga an tafi da kanin mahaifinsa.

“Wannan ne dalilin da ya sa ma ba zai samu halartar zanga-zangar ba. Kin ga kenan shi abin dake faruwa a jihar ya ma shafe shi. “Kuma idan aka shiga irin wannan wuraren ana kashe mutane sannan a tafi da wasu, matansu ma a gaban ‘ya’ya da miji a yi masu fyade, idan an gama ma sai su dibi ruwan batir su watsa wa mace.

Shin mai ya fi wannan bala’i? Kuma ma ina manyanmu na Arewa? Mun ji sun yi shiru. “Kwanan nan naga wani bidiyon dattawan Arewa na nuna gazawar gwamnatin nan, saboda bata cika alkawari, abu na farko ta ce za ta bayar da tsaro amma duk ta gaza. “Kafin ma wannan zanga-zangar mun tura wa hukumomin tsaro cewa za mu yi zanga-zangar lumana ne, akwai kungiyoyi na sa-kai akwai kungiyoyin dalibai da makamantansu, amma daga karshe an nemi a wurga da mutane.

“Maganar da nake yi maka, yanzu haka mintina 41 a ofishin ‘yan sanda a bayan kanta, an kama mu, wanda mun gaya masu abin da za mu yi, amma sai aka kulle hanyoyi, ba a bamu hadin kai ba, wanda ‘yan sanda na lamba daya wajen rashin bamu hadin kai. “Sai dai daga baya sun bamu hadin kai na maganganu, domin shi kansa kwamishinan ya zo, domin da bai zo ba da Shugaban yankin ba zai sake mu ba, an kama mu mu hudu tsawon minti 41.

“Kuma mu zanga-zangar lumana mu ke yi, sannan kuma mu na yin sa saboda talaka ne domin mu talakawa ne, a na kashe mana yan’uwanmu. Akalla mutane 300 zuwa 400 ne su ka fito zanga-zangar tsakanin maza da mata.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: