Jama’ar Nasarawa Za Su Fito Su Tarbi Buhari, In Ji Shugaban Talakawa

Shugaban Talakawan Jihar Nasarawa, Alhaji Usman Adamu Doya 50 yace alumman Jihar Nasarawa za su fito kwai da kwarkwata maza da mata wajen tarban Shugaban kasa Alhaji Muhammad Buhari. Yace muyin yekuwa ga dukanin alumman jihar masu son zaman lafiya tun daga karamar hukumar karu zuwa Lafia da cewa babu bambamcin siyasa kowa ya fito saboda abinda Shugaban kasa zaizoyi ba siyasa bane zai kawoshi zaizone bude ayyukan cigaba da zai amfani alumman wannan jihar baki daya.

Kuma ayyukane na a gani a kasa wanda shikansa Shugaban kasan zaiyi farin ciki da ganin ayyukan day a shafi rayuwar talakawane.

Yace; wannan ziyarar na Shugaban kasa bashine karo na farkoba a wannan Gwamnati ta Alhaji Umar Tanko AL-makura saboda a lokacin Shugaban kasa Jonathan ya taba zuwa wannan jihar inda yazo ya bude wasu ayyuka na cigaba da Gwamna Umar Tanko Al-makura ya samar a wannan jihar. Yace a wancan lokacin akwai bambamcin siyasa tsakanin Shugaban kasa Jonathan da Gwamna Al-makura amma saboda shi Shugaban Kasa na kowa da kowane kuma ya amsa wannan kira ya kuma aka bude wannan ayyukan.

Yace; yanzu wannan Gwamnati ta Al-makura Jam’iyyar dayace dana SHugaban kasa yace; Shugaban Kasa zazone ya bude ayyukan da dukanin Kananan hukumomi guda goma sha uku za su amfana.

Ya ce; dukanin kananan hukumomin da muke dasu a wannan Jihar babu Karamar hukumar da Gwamnatin AL-makura batayi aikin azo a ganiba. Yace Al-makura ya sauya fasalin wannan Jihar. Ta gina mahimman ayyuka a dukannin kananan hukumomi. Yace; an gina hanyoyi da zai hada garuruwa ya raya karkara da birane.

Hanya Asibiti wuta ruwa makarantu kasuwanni. Gakuma wuraren nazarin karatu. Yace; wannan kasuwan da Shugaban kasa zaizo ya bude. Ba wannan Gwamnatin ta sanya tubalin ginataba amma ya kamata ace an kammalashi tuntuni, Shugabannin da suka gabata sai sukayi watsi da wannan kasuwan ta kasa da kasa. Gwamna Al-makura yaga ciwa watsi da wannan mahimmin wurin almubazarancine da dukiyar Jihar Nasarawa kuma wajene da zai kawowa Jihar cigaba. Shiyasa ya sanya hannu ya daure yayi kokari ya kammala ayyukan wannan kasuwan da idan mutum yana kowani Jiharne zaiyi fatan ya samu Shago a wannan kasuwan saboda tana da makotaka da babban birnin tarayya Abuja.

Kuma wannan makarantar da Gwamna Al-makura zai bude makarantace da duk Afirika zata amfani alumma masamman yayan talakawa saboda duk inda kaga Nakassasu mafiya yawa yaran talakawane kuma suke cikin matsala.

To wannan makarantar zata samar ma nakasassau da ayyukan cigaba abashi ilumi a koyar dashi sana’a abashi abinci wannan ba karamin taimakawa talakawa Gwamna Al-makura yayiba kuma irin wannan aikinne Shugaban kasa Muhammad Buhari yake bukata saboda shin a talakawane . Nayi imani zai yaba da rawar gani da Gwamna AL-makura ya taka a ayyukan cigaba a Jihar Nasarawa.

Exit mobile version