Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Jama’ar a jihar Yobe sun bayyana gamsuwar su dangane da canje-canje da tsare-tsaren bangaren kamfanin jaridar Leadership A Yau mai fitowa kullum, irinta ta farko a tarihin jaridun Hausa a Nijeriya. Har wala yau kuma, ra’ayoyin sun kara da cewa, wadannan nasarorin sun samu ne ta dalilan jajircewar shugaban kamfanin da sadaukarwar ma’aikatan ta.
Jaridar Leadership A Yau, a halin yanzu ba tada sa’a a tsakanin jaridun Hausa; idan an yi la’akari da zubi da tsarin ta, sannan da yawan jama’ar da ke bibiyar ta a kowanne bangaren kasar nan. Baya ga wannan kuma, ga yadda take dada yawan masu ribibin ta a hannun dilalai kana da a kafafen sada-zumunta (social media). Muna fatar wannan jarida mai farinjini ta dore.
Wadannan na daga cikin ra’ayoyin jama’a wadanda wakilin mu ya zanta dasu a jihar Yobe, tare da bayyana yadda suke kallon mu a ma’aunin sikeli.
“Sannan a can baya tana fitowa a cikin kowanne sau daya ne, amma yanzu tana fitowa ne a kowacce rana. Haka kuma, a dauri bana zaton tana shiga a cikin lungu da sakon kowanne bangaren kasar nan. Amma yanzu tana shiga kusan kowacce jiha tare da samun wakilai da marubuta daga ko’ina, alal hakika Leadership Hausa ta samu gagarumin ci gaba”. Alhaji Hamisu.
Gefe guda kuma, ya sake nanata cewa “duk wadannan nasarori da ci gaban sun samu ne ta dalilin sadaukarwa da juriyar shugaban kamfanin da ma’aikatan ta a hannu daya kuma muna hasashen cewa jaridar zata habaka ta kasance daya daga cikin jaridu mafi bunkasa kuma masu fada a ji da kasancewa madogara ga al’umma masu amfani da harshen Hausa; matsayin sahihiyar kafar bada ingantattun labarai”.
Shima a lokacin da yake tofa albarkacin bakin shi, Alhaji Babangida Ahmed, Potiskum (Mawalfin jaridar Jekadiya) ya fara da bayyana cewa, jaridar Leadership A Yau ta samu gagarumar tarbar al’ummar jihar Yobe. Ya kara da nuna cewa” bisa hakikanin gaskiya a nan jihar Yobe wannan jarida taku tana samun karbuwa sosai, kuma hakan yana da nasaba da sahihan labaran da kuke bayarwa”. Inji shi.
“Kun kafa tarihi, kuma muna yi muku fatar samun ci gaba da dorewa. Sannan ba abin mamaki bane ace Leadership Hausa ta samu ci gaba ba, saboda na taba sauraron kalaman shugaban kamfanin; Mista Sam Nda-Isaiah dangane da cewa aikin jarida bana dragon mutum bane, saboda haka ku ci gaba da dagewa da jajircewa, akwai karin nasarori a gaba”. Ya bayyana.
Gogaggen dan jaridar ya kara da cewa” babban abinda ya karawa masu bibiyar ku karsashi da kwarin gwiwa wajen dorewa shi ne jerin kwararrun Editoci da Daraktoci da wakilai, sanannun mutane ne wadanda kowa ya san su a kasar nan a fagen sarrafa labarai. Addu’ar mu ita ce Allah yayi musu jagora cikin nasarori”. Inji Babangida.