Jami’ai Da Kwararrun Afirka Sun Yi Maraba Da Amincewar Da Alluran Riga Kafin COVID-19 Na Sinopharm Na Kasar Sin Ya Samu Daga WHO

Daga CRI Hausa

Kwanan baya, alluran riga-kafin annobar numfashi ta COVID-19 na kamfanin Sinopharm na Sin ya samu takardar shaidar amfanin gaggawa daga hukumar WHO. Jami’ai da kwararrun kasashen Afirka sun yi maraba game da haka.

Ahmed Ogwell, Mataimakin Daraktan Cibiyar Kula da Rigakafin Cututtuka ta Afirka, ya fada a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Asabar cewa, alluran riga-kafin na Sinopharm na kasar Sin sun samu tabbaci daga hukumar WHO don yin amfani da shi cikin gaggawa, wanda ya kasance labari ne mai kyau ga kasashe da jama’ar da annobar ta addaba, kuma an bayar da wata damar zabi ga shirin aiwatar da allurar rigakafin COVID-19 na COVAX da hukumar WHO ke jagoranta da kuma kasashen da ke fama da karancin allurar rigakafin.

Ya kara da cewa, Cibiyar Kula da Rigakafin Cututtuka ta Afirka zata ci gaba da hada kai tare da masu samar da allurar rigakafin, ciki har da Sinopharm, don tabbatar da cewa Afirka zata iya samun alluran riga-kafi masu inganci da amfani da kuma araha, hakan za a iya cimma burin yin rigakafin ga ‘yan Afirka a kalla da kashi 60%.

Ministan Kiwon Lafiya na kasar Zambiya Jonas Chanda ya bayyana a jiya Asabar cewa, an riga an tabbatar da cewa, riga-kafin Sinopharm ya zama riga-kafi mai amfani da inganci. Gwamnatin kasarsa za ta yi la’akari da shigar da alluran riga-kafin Sinopharm, don tabbatar da yiwa mutane mafi yawa allurar rigakafin. (Mai fassara: Bilkisu)

Exit mobile version