Daga Sulaiman Ibrahim
Rundunar jami’an ‘yan banga ta Amotekun sun bayyana nasarar kama mutum biyu da ake zargi ‘yan garkuwa da mutane ne a jihar Ondo.
‘yan bangar sun kuma ceto mutum uku matafiya da akayi garkuwa dasu akan hanyar Ifira-Akoko/Idoani da ke karamar hukumar Ose daga hannun masu garkuwa da mutanen.
“Matafiyan su ne Adewale Adebisi, Ahan Mary, da kuma Ladi Bude, wadanda ‘yan bindigar suka sace a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Akure dake Ondo daga Benuwe a safiyar Asabar,” a cewar rundunar ta Amotekun.
Rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun tsare hanyar ne sannan suka umarci mutanen su fito daga motocinsu daga nan suka shiga da su daji