Umar A Hunkuyi" />

Jami’an DSS Su Na Tsare Da Wani Malamin Addinin Musulunci A Katsina

An zargi Jami’an hukumar tsaro na DSS a Katsina, da gayyatar wani malamin Addinin Musulunci Ofishinsu, sannan kuma sai suka tsare shi, Malamin mai suna, Malam Aminu Usman, wanda aka fi da kira da, Abu Ammar, an tsare Abu Ammar ne a ranar Talata, wasu majiyoyi suka ce tsare shin ba zai rasa nasaba da wani wa’azi da ya gabatar a ranar Juma’a kafin zuwan Liman, wanda a cikin wa’azin na shi ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari a kan abin da ya kira da nuna halin ko-in-kula ga tabarbarewar tsaro a sassan kasar nan.
Wakilinmu ya ba mu rahoton cewa, Abu Ammar, yana tare da abokinsa ne mai suna Malam Shamsu, inda ya amsa wani kira daga jami’an hukumar tsaron na DSS, kan ya kai kansa ofishin nasu na Jihar. Ya kuwa amsa kiran, suka kuma tafi tare da abokin na shi, bayan dan wani lokaci ne sai jami’an DSS din suka umurci abokin na shi Malam Shamsu da ya kama gabansa dab da lokacin shan ruwa a jiyan,” in ji majiyar.
danshi mai suna Murtala, ya tabbatar da kamun mahaifin na shi a lokacin da wakilin namu ya ziyarci gidan na su da ke Filin Samji, a cikin garin na Katsina, a ranar Laraba. Ko da wakilin namu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isah, domin jin ta bakin rundunar, cewa ya yi a yanzun yake jin wannan labarin. In dai ba a manta ba, a watan Maris, 2015, jami’an hukumar tsaron na DSS sun taba yi wa Abu Ammar irin wannan kamun.

Exit mobile version