Daga Mustapha Ibrahim Tela, Kano
Da alamu jami’an Gwamanti ne kawai suka amfana da tafiyar da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar zuwa ƙasar Sin wato Chana, amma ba yan kasuwa ba duk da an ce tafiya da aka yi ta don bunƙasa harkar kasuwanci tsakanin kano da ƙasar Chana.
Al’amarin bai yi wa da yawa daga cikin ‘yan kasuwar Kanon daɗi ba, saboda ganin yadda aka cusa Kwamishinoni da muƙarraban gwamnati a tafiyar.
Wanda hakan ya nuna cewa ko yanzu sun ci gajiyar wannan tafiya kuma su ne za su amfana da ita.
ya ce, yaya za’a yi ace za’a yi tafiya irin wannan domin bunƙasa kasuwanci a Kano, amma ba’a ɗauki ɗan kasuwar Kantin kwari ba, kuma ba’a ɗauka a kasuwar Sabon gari, ko Singa, ko Kurmi, a ɗayan kasuwannin kano ba, to ina maganar bunƙasa kasuwa?
Ai kamata yay i ace a ƙalla ko wace kasuwa a ɗauki mutum ɗaya ya wakilce ta daga cikin ‘yan ƙungiyar kasuwanni, domin ɗan kasuwa shi ya san me ye kasuwanci kuma ya za’ayi a kasuwa a ci riba abu ya bunƙasa.
Amma ba ka ɗaɓi tawagar Kwamishinoni kuma kana maganar kasuwa ba, mu a wannan tafiyar muna ganin Kwamishinoni ne da gwamna kawai su ka ci amfanin wannan tafiya ta gwamnan Kano zuwa ƙasar Sin a cewar Alhaji Sagir Sharu Wada Dandago Kano.
Haka kuma ya koka da a yadda ‘yan siyasa su ka lalata kasuwanci suka jefa ‘yan kasuwa cikin wani hali ta yadda Dala ta yi tsada kuma su ‘yan siyasa ba su damu da ‘yan kasuwa ba komai ba’a tuntuɓarsu sai dai kawai ayi son rai na ‘yan siyasa.
Don haka ne ma ya ce abinda ‘yan siyasa suke musu a yanzu ‘yan kasuwa sun gama shiri tsaf za su koya wa ‘yan siyasa darasi a zaɓen 2019 in Allah ya kaimu, domin duk wani ɗan siyasa ‘yan kasuwa ne ke taimaka masa ya hau, amma yanzu ba ruwansu da ‘yan kasuwa a kowane mataki.
A shekaru 57 da Nijeriya ta yi da samun ‘yancin kai ‘yan kasuwa ba su gamsu da yadda masu mulki suke tafi da al’amuran kasuwanci ba, saboda haka in dai ana so ayi ɗan kasuwa to wajibi ne duk wani minista da za’a ba harkar da ta shafi yan kasuwa to ya zama ɗansu ne daga kasuwa, ya san kasuwa kuma ya san matsalolin ‘yan kasuwa in ko ba haka ba to su sun san kawai ba kishinsu ake ba a cewar Sharu Wada Ɗandago.
Sai ya ce wannan maganar siyasa ce domin an tafi da ɗaya daga cikin sanannun ‘yan kasuwar Kano Alhaji Isyaku Umar Tofa ɗan Adalan Kano don ba zai yiwu a ce sai an ɗabi duk ‘yan kasuwa an tafi da su ba.