Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da rahoton cewa, tun bayan da aka shirya babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis a shekara ta 2012, ya zuwa yanzu, kasar ta tura wasu jami’an kimiyya da fasaha da yawansu ya tasam ma dubu 290 zuwa sassa daban-daban, inda suka taimaka sosai ga samar da hidimomin kimiyya da fasaha da raya sana’o’i a kauyuka masu fama da talauci kusan dubu 100.
Shugaban kungiyar kimiyya da fasaha ta lardin Yunnan, Mista Zhu Youyong yana daya daga cikinsu, ya kuma bayyana cewa, sun bullo da kwasa-kwasai na horas da fasahohi, da koyarwa a gonaki.
Manoman da suka gama karatu, dukkansu sun fita daga yanayin talauci, kuma kusan rabinsu sun taimakawa ‘yan uwa da abokanansu fita daga talauci, har ma akwai kaso 10 bisa dari daga cikinsu wadanda suka taimaki daukacin mazauna kauyensu fita daga yanayin talauci.
Zhu Youyong, wanda ya jima yana aikin tallafawa matalauta a yankunan karkara dake garin Zhutang na gundumar Lancang ta birnin Pu’er dake lardin Yunnan, shi da tawagarsa sun yi tattaki zuwa sassa daban-daban a wurin, a wani kokari na taimakawa jama’a yaki da fatara da kyautata rayuwarsu ta hanyar kimiyya da fasaha. (Mai Fassara: Murtala Zhang)