Sulaiman Ibrahim" />

Jami’an Kwastan Sun Kama Mota Shake Da Makamai A Jihar Kebbi

Jami’an hukumar hana fasakwauri Kwastan sun kama wata babbar mota shake da bindigogi kirar hannu a karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Harsashe kenan da aka kama

Mai magana da yawun hukumar Kwastam ta Nijeriya, Joseph Attah shi yasawa sanarwar hannu, inda ya kara da cewa an kama mutum uku dake tare da motar kuma tuni aka fara bincike kan makaman.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a yammacin Lahadi, inda ta ce bindigogin da aka kama suna cikin buhunhuna ne, adadinsu sun kai guda 73 da harsashi 891.

Kwamanda mai kula da yankin Zone B, Hamisu Albashir ya bayyana cewa wannan kamen izina ce ga duk mai yinkurin shigowa da makamai cikin Nijeriya ta yankin Zone B cewa ba za suyi nasara ba.

Ya kuma kara kira musamman ga mazauna yankin iyakokin kasar nan da su dinga kaiwa jami’an tsaro rahoton masu fasakwari.

Exit mobile version