Rabiu Ali Indabawa" />

Jami’an Kwastom Sun Kwace Kayan Naira Miliyan 91 A Iyakar Seme Cikin Makonni Biyar

Kyautta rufe bakin iyaka, Yankin Seme na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ya yi nasarar kama mutane 235 tare da biyan diyyar Naira 91,162,942 a cikin makonni biyar.

Wadanda ke cikin kamun suna da bas guda biyu mallakar kamfanin Chisco Nigeria Limited na dauke da magunguna marasa inganci.

Sauran abubuwan da aka kwace sun hada da jakunkuna 1113 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50k, lita 24,710 na Premium mota;  kayayyakin kaji 188; Kayan kwalliya 105; Motoci 22; Sutura 84 na riguna, jakunkuna na mata da takalma.

Sauran kayan sun hada da jakunkuna 30 da kuma kwalin sabulu katon 35 na alawar cakulan, kayan babur guda 51, kayan jiguna 28 na man kayan marmari, jakunkuna 25 na furtsatse da fata.

Bugu da kari an sake kwace wasu kayan da suka hada da jakunkuna 10 na guna (egusi), guntu 89 na bakin ruwa da magarine, jakunkuna biyu na kifi, fakitoci 12 na gyada da kuma guntun takardu 23.

Jami’in kula da Yankin Kwastam na rundunar, Dalha Cheidi Wada, ya ce yankin ba zai kasance wurin masu fataucin mutane da sauran masu aikata laifi ba.

Ya ce, an kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a wasu abubuwa daban-daban da aka kama, yayin da biyu aka mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), uku sun samu beli.

A cewar Wada, an gano motocin Chisco dauke da sinadarin amphetamine.

Ya yi bayanin cewa ya yi ban da keta dokar hana fita a kan iyaka, wanda ya hana shigowa da fitarwa zuwa ciki da wajen Nijeriya, magungunan an shigo da su ba tare da lambar rajista da Hukumar Kula da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ba.

Wada ya ce, motocin su na dauke da katon guda 13 da 29 da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 6 ban da na 422,500mg na tramadol.

“Jami’an mu na sa ido a ko da yaushe suna cikin shiri domin ganowa da kuma dakile abubuwan da aka sata a cikin su. A cikin ɗayan lamari, masu fataucin mutane sun nuna matsayin sarki na gargajiya don jin daɗin girmamawa ta sarauta da wucewa kyauta. Bayan da a ka neme shi da ya bude but na motar, ya san kuma wasan ya tashi, ya yi wuf ya sauka daga motar ya ranta a na kare ya gudu zuwa daji.

“Mun kwace motar da abubuwan satar da ke ciki. Har ila yau, a na hako kayayyakin yau da kullum na man fetur kuma muna kama su ta hanyoyi daban-daban na daji. Mu na tabbatar da cewa babu wanda ya saci jarka na PMS. Yayin da mu ke magana, karin rarar man fetur ya shigo, don tabbatar da abin da na fadi da farko, ” a cewar Wada.

Exit mobile version