Daga Khalid Idris Doya,
Jami’an lafiya 476 da suka hada da Likitoci, Nas-nas, kwararru kan harhada magunguna, jami’an dakunan gwaje-gwaje, direbobi da sauran ma’aikatan lafiya ne suka kamu da cutar Korona tun lokacin da aka samu kes din farko a cikin babban birnin tarayya (FCT) Abuja kamar yadda aka nakalto jiya.
Anthony Ogunleye, babban sakataren watsa labarai na Ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT) Muhammed Bello, shine ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ya fitar.
Ya ce zuwa yanzu babu wani jami’in lafiya yake kwance domin jinya a halin yanzu.
Ya ce tun lokacin da annobar cutar ta barke hukumomi a babban birnin tarayya suka tashi tsaye domin tabbatar da dakile yaduwar cutar, wanda kuma ya ce sun cimma muhimman nasarori kan hakan.
Ya ce sun samar da kwamitocin tabbatar da gwaje-gwaje bisa shawarorin da hukumomin lafiya da NCDC suka bayar.
Ya ce yanzu haka jami’an lafiya da asibitoci sun dawo bakunan ayyukansu gadan-gadan tun bayan hutun kirsimeti domin ci gaba da bada gudunmawa wajen rage kaifin yaduwar cutuka.