Shirin yaƙi da safarar bil’adama da fasa-ƙwaurin ‘yan gudun hijira (A-TIPSOM) ya shirya horaswa ta kwana uku ga manyan jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS).
Shirin wanda Tarayyar Turai (EU) da Gidauniyar Harkokin Mulki da Tsara Manufofi ta Amurka (FIIAPP) ke ɗaukan nauyinsa, ya shirya horaswar ce a matsayin wani muhimmin sashe na ayyukan da yake gudanarwa.
Galibin masu halartar horaswar jami’ai ne masu horaswa a manyan cibiyoyin bayar da horo na NIS, sai kuma wasu da aka zaƙulo daga shalkwatar hukumar da kuma babban ofishinta na shiyyar Abuja. Waɗanda suke samun horon, an zaƙulo su ne bayan an darje domin tabbatar da cewa ilimin da suka samu sun koyar da sauran jami’an da suka dace.
Babban burin horaswar shi ne tabbatar da cewa mashu halartar sun samu cikakken ilimin da ake buƙata wajen gudanar da ayyukansu, bisa la’akari da dokokin shige da fice na shekarar 2015 da kuma na 2017 waɗanda suke da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da ayyukan hukumar na yau da kullum.
Da yake gabatar da saƙonsa na fatan alheri a matsayin babban baƙo a wurin horaswar, Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede MFR ya bayyana muhimmancin kowa a cikin mahalartan ya buɗe zuciyarsa tare da aiki da dokokin shige da fice na 2015 da na 2017 domin amfanin hukumar da kuma ƙasa bakiɗaya. Ya ƙara da cewa duk wani abu da jami’in hukumar zai aikata akwai ta inda zai iya yin tasiri ga kula da shige da ficen ƙasa, da bayar da biza da kula da kai-komon jama’a.
Shugaban hukumar ya sake nanata buƙatar samar da muhimman dabaru na yaƙi da manyan laifuka kamar safarar bil’adama da fasa-ƙwaurin ‘yan gudun hijira.
Bayan kammala jawabin, sai CGI Babandede ya buɗe taron. Shugaban tawagar Shirin na A-TIPSON ya samu wakilcin babban jami’in gudanarwa na shirin, Mista Jose Nsang Andeme.
Idan dai ba a manta ba, an gudanar da taron ƙara wa juna ilimi a kan dokokin shige da ficen ƙasa na 2015 da na 2017 ga manyan jami’an NIS a ranakun 8 da 9 ga Disambar 2020, sa’ilin da aka tsara gabatar da taron karo na biyu daga ranar 18 zuwa 20 ga Janairun 2021 domin ƙara gyagije mahalartan game da ilimi da aiki da dokokin.
Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja
Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...