Jami’an Siyasa Da Masanan Kasashen Afirka Na Fatan Ganin Taron Dakar Zai Inganta Hadin Gwiwar Afirka Da Sin Zuwa Wani Sabon Matsayi

Masanan Kasashen Afirka

Daga CRI Hausa,

Daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Nuwamba, za a gudanar da taron ministoci karo na 8, na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

A yayin da suke zantawa da ‘dan jaridar babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, manyan jami’an siyasa, da masana na kasashen Afirka masu dama sun bayyana cewa, tun bayan kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a shekaru 21 da suka gabata, ya ba da gudummawa mai kyau ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummun Afirka, ana kuma sa ran ganin taron na Dakar zai gabatar da wani sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin, da kuma samar da wani sabon kuzari a dangantakar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

Onunaiju Charles Okechukwu, darektan cibiyar nazarin kasar Sin a Najeriya, yana ganin cewa, ya kamata a mayar da more fasahohin da kasar Sin ta samu a gudanar da harkokin mulkin kasa, ya zama wani muhimmin sashe na ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin a nan gaba. Ko da yake ba za a iya yin kwafin nasarar da kasar Sin ta samu ba, amma ayyukan kasar Sin sun cancanci a yi koyi da su.

A cewarsa, “Koyo daga kasar Sin yana nufin koyon yadda ake neman hanyar samun ci gaba mai dacewa da yanayin kasa, da kuma kara amfani da karfin jama’a, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa.”

Mataimakin darektan ofishin yada labarai na gwamnatin kasar Tanzania Rodney Mbuya ya bayyana cewa, taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, ya samar da halin samun moriyar juna da samun nasara tare, kuma ta haka ne amfanin gonan kasar Tanzaniya ya samu damar shiga kasuwannin kasar Sin. A hannu guda kuma kamfanonin kasar Sin su ma sun zama ginshiki a kasuwar kwangilolin injiniya ta kasar ta Tanzaniya. Ya kuma yi fatan taron Dakar zai kara inganta daidaita ajandar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin, da ajandar kungiyar tarayyar Afirka ta kafin nan da shekarar 2063.

(Mai fassara: Bilkisu)

Exit mobile version