Jami’an tsaro a gabashin Jamhuriyyar Dimukradiyar Congo sun bindige ‘yangudun hijirar Burundi fiye da mutum talatin har lahira. Rahotanni sun nuna cewa, daga lardin Kibu ta Kudu wasu ‘yan gudun hijirar da dama sun jikkata, sannan kuma an kashe wani dan sanda guda daya. Jami’ai a kasar sun ce ‘yan kasar ta Burundi goma sha takwas ne aka kashe. Sannan wata majiya ta ce jami’an tsaron Congo din sun budewa ‘yan gudun hijirar wuta ne bayan sun danna cikin wani kurkuku, inda ake tsare da wasu ‘yan kasar Burundi su hudu. Dubban daruruwan ‘yan kasar Burundi ne suka gudu daga kasarsu lokacin da tashin hankali ya barke a shekarar 2015, bayan shugaba Pierre Nkurun ziza ya yanke shawarar neman shugabancin kasar a wa’adi na uku.
Me Zai Biyo Bayan Darewar Karajar Biden Da Faduwar Trump?
Idanun duniya na kan ranar Larabar jiya, 20 ga Janarairu,...