Jami’an tsaro sun kama wani karamin yaro dan shekara 10 kacal mai suna Monday Omoruye, wanda ke zaune a titin Ring Road da ke Jihar Edo, saboda shigarsa cikin ayyukan aikata laifin da aikata ya hada da fashi da makami.
A cikin wani faifan bidiyo wanda yanzu ya yadu a yanar gizo, Monday ya bayyana cewa, dan uwansa ne ya sanya shi a harkar fashi, kuma zuwa yanzu ya gudanar da ayyukan fashin sau hudu.
Lokacin da aka tambaye shi daga ina ya samo makamansa, sai ya ce yayin zanga-zangar #EndSARS na shakarar 2020, shi da dan uwansa da wasu abokansu sun kutsa kai ofishin ’yan sanda na kasuwar Oba inda suka yi awon gaba da makamai daga ofishin.
Da yake ci gaba da magana, Monday ya ce, dan uwan nasa ya koya masa yadda ake harbi da bindiga, kuma zuwa yanzu ya kashe mutane biyu a yayin da suke aiwatar da wani fashi.
“Akwai wani mutum, ban sani ba ko ya buge yake, ya ba mu wayarsa, muka mayar da ita. Ya fadawa dayan mutumin cewa yana son barci, sai muka ce masa kar ka barshi ya yi barci saboda wancan zai saci komai, kudi da wayoyi, mutumin bai saurara ba. Lokacin da gari ya waye ne na ce kar ku ba shi wayarka, amma bai saurara ba, dayan ya ce masa yana son saukar da wakoki da yawa a wayar, amma ya gudu don haka muna nemansa, kuma mai wayar ya ce idan ba ya ganinsa, zai rike ni, shi ya sa ya rike ni, ya kira min ‘yan banga. Yayana yana da bindigogin ‘yan sanda guda biyu da ya sace daga ofishin ‘yan sanda a kasuwar Urban yayin zanga-zangar #EndSARS,” in ji Monday.
Ya ci gaba da cewa, “Zan iya amfani da karamar bindiga, dan uwana ya koya min kuma yana rike su duka. Na bi su har sau hudu yin fashi a Sapele, hanyar Siluko, Sakpoba. Mun kashe mutane 2, daya a hanyar Siluko, dayan kuma a Kasuwar Igan. Ban san sunayen wadanda muka kashe ba, domin da mungama fashi muke guduwa. Idan yana son ganin dan uwana, sai an tafi da safe da misalin karfe 8 na safe, za a ganshi.”