Jami'an Tsaro Sun Kama Ɗan Bindigar Da Ake Zargi Da Kashe Nabeeha
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an Tsaro Sun Kama Ɗan Bindigar Da Ake Zargi Da Kashe Nabeeha

byMuhammad
2 years ago
Nabeeha

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan bindiga wanda ake zargi da kashe matashiyar nan Nabeeha da kuma garkuwa da wasu.

TRT Afrika Hausa ta rawaito cewa, Rundunar ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce ta kama ɗan bindigar a wani otel da ke garin Tafa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

  • ‘Yan Uwan Marigayiya Nabeeha Su 5 Da Ɓarayin Mutane Suka Sace Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci
  • A Ceto Sauran Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su Daga Ukuba, In Ji Iyalan Al-Kadiriyah

A sanarwar, ta ce ɗan bindigar mai shekara 28 mai suna Bello Mohammed asalin ɗan jihar Zamfara ne kuma an kama shi da zunzurutun kuɗi har naira miliyan 2.25, inda ake zargin kuɗin fansa ne da ya karɓa.

“Wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa yana daga cikin gungun waɗanda suka yi garkuwa da wani Barista Ariyo a unguwar Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairun 2024, inda suka kashe wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, daga ciki har da Nabeeha, wadda ƴa ce ga lauyan, a ranar 13 ga watan Janairun 2024 a sansanin masu garkuwan da ke Jihar Kaduna.

“Wanda ake zargin, a cikin wani yanayi mai ban mamaki, ya bayar da naira 1,000,000 (Naira miliyan daya kacal) don jawo hankalin DPO, wanda ya ki amincewa da tayin, inda ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne runduna ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da kuɓutar da ƴan uwan Nabeeha waɗanda ke hannun ƴan bindiga.

An sace ‘yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.

Sai dai daga bisani ‘yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka bukaci ya nemo N60m a matsayin kudin fansa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Next Post
Rashin Kishin Kasa Da ‘Yan Kasa A Kasafin Kudin Nijeriya Na 2024

Rashin Kishin Kasa Da ‘Yan Kasa A Kasafin Kudin Nijeriya Na 2024

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version