Bello Hamza" />

Jami’an Tsaro Sun Kama Buba Galadima

A jiya Lahadi ne, jami’am tsaro suka cafke Buba Galadima mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Daya daga cikin yaran Alhaji Buba Galadima ne ta tabbatar wa da manema labarai kamun da aka yi wa mahaifin nasu, in da ta ce, jami’an tsaron sun biyo Buba Galadman ne har zuwa unguwar Wuse 2 in da suka shigar da shi wata mota mara lamba suka kuma yi awaon gaba da shi wurin da har yanzu ba a san ko ina bane.
Tun da farkon ranar Lahadin ne, mai magana da yawun kungiya yakin neman zaben Shugaba Buhari, Festus Keyamo, ya bukaci a kama Mista Galadima a bisa laifin ayyana dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.
“Muna kira ga INEC da hukumar NBBC da kuma jami’an tsaro da su gargadi jami’iyyar PDP da mutanen su a kan sanar da sakamakon zabe koma bayan wanda hukuma za ta bayar, bai kamata a zura wa jami’yyun adawa ido suna karya dokokin zabe ba, ba tare da an hukunta su ba, musamman irin kungiya CUPP da sauransu.

“Don shirya wa wannna mummuna tsarin nasu har wasu kafafen su na intanet sun fara gabatar da sakamakon zabe dake nuna cewa, jam’iyyar PDP ta lashe zaben, Alhaji Buba Galadima, wanda ke magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar ya sanar a wani faifan bidiyon da ya fitar inda yake sanar da cewa, jam’iyyar PDP ta lashe zaben da aka gudanar, wai kuma yana magana ne da yawun Alhaji Atiku Abubakar. A kan haka muke kira da a gagauata kama shi tare da hukunta shi, muna kuma kiran Atiku Abubakar ya yi magana a kan faifan bidiyon da Alhaji Buba Galadima ya gabatar.
“A kan haka muke kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da wakilan kasashen waje da kuma jam’iyyun ‘yan adawa masu imani su kai zuciya nesa tare da hana irin wadannan bata garin, dole Nijeriya zai ci gaba da wanzuwa har bayan zaben da ake gudanarwa.
“A shekarun da suka gabata an sha ayyana jam’iyyar PDP a mastayin jam’iyyar data lashe zabe a yanayi na rudani. A wadanan lokutta, Shugaba Muhammadu Buhari bai taba daukan doka a hanunsa ba, ya kan nufi kotu ne don mika korafinsa.
“Wannna shiri na baya bayan nan yana nuni ne da cewa, jam’iyyar PDP ba ta dauki wani darasi ba suna kuma son lashe zabe ne ko ta ko wanne hali,” inji Mista Keyamo.

Exit mobile version