Sagir Abubukar" />

Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Shida Da Ceto Mata 17 Da Yara Shida

Da misalin karfe biyu da rabi na daren Talata, ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari a garin Lambo, da ke gundumar Wurma a karamar hukumar Kurfi, ta jihar Katsina,inda suka kashe mutane biyu da kuma sace Mata goma sha bakwai da kananan yara shidda da sace dabbobi guda saba’in da hudu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyana haka, a wata takardar manema labarai da ya raba ya sanya hannu a Katsina.

Gambo Isa ya ci gaba da cewa an ankarar da jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojojin kasa da na sama, inda suka hanzarta suka toshe hanyar da za su wucea, suka yi wa yankin kawanya, a tsakanin garin Ummadau zuwa Kwayawa, wanda ita ce hanyar da za su bi, su shiga daji, inda suka yi ba-ta-kashi, wanda ya yi sanadiyyar kashe ‘yan bindiga shidda.

An kuma kubutar da Mata da kananan yara wadanda suka sata su ashirin da ukku, an kuma kwato shanu ashirin da ukku da tumaki ashirin da awaki talatin da daya da mashina goma sha biyu da kuma wata bindiga kirar G3 a hannun su. A na cigaba da bincike.

 

Exit mobile version