Jami’an Tsaro Sun Kubutar Da Wasu Daliban FGC Yawuri

Rahotanni daga jihar Kebbi arewa maso yammacin Nijeriya na cewa sojoji sun kubutar da wasu daga cikin yara ‘yan makarantar Gwamnatin Tarayya ta garin Birnin Yawuri da aka sace. Rahotannin sun ce sojojin sun yi wa barayin kofar rago ne a ranar Alhamis da daddare a cikin daji.

Dan majalisa mai wakilar Yawuri a majalisar dokokin Kebbi Honorabul Muhammad Bello Ngaski ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin. A jiya Alhamis da rana ne ‘yan bindigar suka kutsa makarantar tare da sace yaran.

Shaidun sun ce an yi gumurzu sosai tsakanin dakarun tsaro da barayin dajin a karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbin. Sun kara da da cewa sojojin sun katse wa barayin hanzari ne ta hanyar yi musu kwanton ɓauna a hanyar tafiya da yaran da suka sata zuwa maboyarsu.

Exit mobile version